'Yan bindiga sun kashe mutum hudu sun tayar da kauye 17 a Sakkwato 

'Yan bindiga sun kashe mutum hudu sun tayar da kauye 17 a Sakkwato 
'Yan bindiga dauke da makamai sun shiga kauyen Bimasa a karamar hukumar Tureta a jihar Sakkwato sun kashe mutum hudu sun jikkata Wasu da dama a daren jiya Laraba.
Daya daga cikin jagorori a kauyen ya yi wa Aminiya karin bayani ya ce a daren jiya(Laraba) da karfe 12:40 barayi suka shigo kauyen saman babura suna da yawa sun fi mutum 10 anan take suka rika harbi kan mai uwa da wabi kai tsaye suka harbi mutum biyar, hudu suka rasu an kai ɗaya asibiti.
"A haka suka rika harbi ta ko'ina, sun buge shagunan mutane suka kwashe wayoyi a wurin masu caji, shagunan da ke sayar da abinci suka saci abinci da yawa, a lokacin ba su yi garkuwa da kowa ba, suka tafi abinsu."
Ya ce a dukkan karamar hukumar 'yan bindigar sun matsa musu kan haka a yanzu sama da gari 17 duk sun tashi sun dawo cikin hidikwatar karamar hukuma ta Tureta a kudu da arewa duk an bar noma domin tsoron 'yan bindigar  kana zuwa gona ana sace ka.
" A yanzu garin Kwarare,Gidan batare, Kaura, Galadimawa, Ci da sha, Rafin gora, Kuruwa Birni, Dantayawa da sauransu, ba kowa 'yan bindiga ke yanda suke so a wuraren.".
Ya roki shugaban karamar hukuma da su yi wata hobbasa da jami'an tsaro don ganin an samu sauki musamman mutane na yin noma.
A kullum mutanen yankin cikin fargaba suke ta 'yan bindiga, abin tausayi da zaran Magrib ta doso mutane za su fara barin gidajen su zuwa wani wurin boyo don kawai su tsira daga harin 'yan bindiga, koyaushe haka ake yakamata gwamnati ta yi wani abu a lamarin.
Wata majiyar ta ce sun kashe mutane hudu amma sun jikkata mutane sun fi 20 wasu na asibitin Tureta wasu na gida suna jinya.
Ya ce shugaban ƙaramar hukumar Honarabul Abubakar Aliyu Tureta ya jajanta masu kan halin da ya same su tare da alkawalin tallafawa wadanda suka samu rauni a harin.
Wakilinmu ya tuntubi shugaban karamar hukumar Tureta kan lamarin amma ba a samu magana da shi ba domin ba ya kusa da waya a lokacin da aka kirasa kuma bai mayar da amsar sakon da aka tura masa ba.