Home Labarai Yan bindiga sun kashe mutum  6  a Sokoto

Yan bindiga sun kashe mutum  6  a Sokoto

10
0



‘Yan bindigar Lakurawa  sun kashe mutane a garin Baidi a karamar hukumar Tangaza a jihar sakkwato a daren Laraba data gabata a wani hari da suka kai a yankin.

Shedun gani da ido ya ce ‘yan bindigar sun shigo ƙauyen suna harbi kan mai uwa da wabi da zimmar samun mutanen garin a haka suka yi nasarar kashe mutane shida.

Yankin na Tangaza wanda ya haɗa Binji da Gudu da Silame da wani yanki na jihar Kebbi suna shan baƙar wuya ga ‘yan bindigar Lakurawa a tsakanin iyakokin.

Wani jami’i a ƙaramar hukumar Tangaza ya tabbatar da faruwar lamarin tare da kira ga Mutanen garin su kwantar da hankali domin Jami’an tsaro suna ƙoƙarin dawo da zaman lafiya a yankin.

Mazauni yankin ya ɗaura alhakin farmakin ne saboda mutanen Baidi da Sanyinna sun ƙi yin biyayya ga dokokin ‘yan bindigar don su ba hukuma ba ne da dokar ƙasa ta aminta a yi wa biyayya.

“Wannan ba shi ne karon farko da suke kawo farmaki a ƙauyen ba, su kashe mutane su gudu,” a cewarsa.

‘Yan bindigar a kwanan baya sun kashe mai garin Sanyinna.

Ya yi kira da jami’an tsaro su tashi tsaye su magance matsalar tsaro a yankin.

An yi wa mutanen da aka kashe sutura an binne su a ranar Alhamis bisa karantarwa addinin musulunci.

Mutanen yankin suna cikin baƙin ciki kan yadda ‘yan bindigar suke addabar su da kashi da yin garkuwa ko kuma tarwatsar da su a garinsu na haihuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here