Home Uncategorized ‘Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya tare da sace mutum shidda a...

‘Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya tare da sace mutum shidda a Sokoto

5
0

‘Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya tare da sace mutum shidda a Sokoto




Mai magana da yawun hukumar ‘yan sandan jihar Sokoto ASP Sanusi Abubakar ya tabbatar da kai harin ‘yan bindiga a jiya jumu’a da marece.

“Mun samu rahoton harin ‘yan bindiga a garin Tangaza ƙaramar hukumar Tangaza a jihar Sokoto da marecen jumu’a.”


“Maharan sun kashe wani mai sana’ar tireda sun yi garkuwa da mutane da har yanzu ba a san adadinsu ba, kuma sun kwashi abinci da kayan sha irinsu lemun gwangwani da roba.

“Haka ma ‘yan sanda da haɗin kan jami’an tsaro suna kan binciken lamarin”, a cewarsa.

Kwanakin nan ‘yan bindiga sun matsawa yankunan jihar Sokoto akwai buƙatar jami’an tsaro su ƙara hoɓɓasa kan lamarin.


Masu bibiyar lamurran a yau da kullum suna danganta ƙarin hare-hare nada nasaba da yanda jami’an soji ke fatattakar maharan a jihar Zamfara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here