'Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya tare da sace mutum shidda a Sokoto
Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar Sokoto ASP Sanusi Abubakar ya tabbatar da kai harin 'yan bindiga a jiya jumu'a da marece.

"Mun samu rahoton harin 'yan bindiga a garin Tangaza ƙaramar hukumar Tangaza a jihar Sokoto da marecen jumu'a."
"Maharan sun kashe wani mai sana'ar tireda sun yi garkuwa da mutane da har yanzu ba a san adadinsu ba, kuma sun kwashi abinci da kayan sha irinsu lemun gwangwani da roba.
"Haka ma 'yan sanda da haɗin kan jami'an tsaro suna kan binciken lamarin", a cewarsa.
Kwanakin nan 'yan bindiga sun matsawa yankunan jihar Sokoto akwai buƙatar jami'an tsaro su ƙara hoɓɓasa kan lamarin.
Masu bibiyar lamurran a yau da kullum suna danganta ƙarin hare-hare nada nasaba da yanda jami'an soji ke fatattakar maharan a jihar Zamfara.
managarciya