'Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya da yin garkuwa da mutum 9 a Sokoto
'Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya da yin garkuwa da mutum 9 a Sokoto
'Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya tare da yin garkuwa da mutum tara a ƙauyen Wababe.
Harin da 'yan bindigar sun kai shi a cikin dare a ranar Talata data wuce.
Majiyar ta shedawa Managarciya maharan sunnshare awa biyu cikin ƙauyen na Wababe a ƙaramar hukumar Dange Shuni a jihar ta Sokoto.
Ya ce a lokacin 'yan bindigar ke cikin ƙauyen da yawan mutane sun gudu sun shiga daji.
Jami'in hulɗa da 'yansanda Sokoto ASP Sanusi Abubakar ya tabbatar da farmakin.
managarciya