'Yan bindiga sun kashe hadimin Gwamnan Katsina
Jaridar LEADERSHIP ta rawaito rundunar ƴan sandan jihar Katsina na tabbatar da mutuwar hadimin Gwamnan jihar, Sanusi Gyaza.
Rundunar ta bakin jami'in hulda da jama'a nata, Abubakar Sadiq ta tabbatarwa da manema labarai cewa, yan bindiga sun kashe hadimin gwamnan.
Ƴan bindigar sun kashe Gyaza da daya daga cikin matansa a gidansa dake garin Gyaza a karamar Kankia a ranar Juma'a.
Rahotanni sun ce a yayin harin, ƴan bindigar sun sace matarsa ta biyu.
Lamarin dai ya haifar da fargaba ga al'ummar yankin dake fama da ayyukan ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa.
managarciya