'Yan Bindiga Sun Kashe Basarake da Wasu 2, Sun Sace  70 a Neja

'Yan Bindiga Sun Kashe Basarake da Wasu 2, Sun Sace  70 a Neja

 

Mutane uku ciki har da Magajin gari sun rasa rayukansu yayin da aka sace wasu 70 a wasu ƙauyukan kananam hukumomin Munya da Paikoro, jihar Neja. 

The Nation ta ce Basaraken garin Beni na cikin waɗanda aka kashe, haka nan an kashe ɗan Magajin Garin Kwagana da kuma wani bawan Allah a kauyen Adunu, ƙaramar hukumar Paikoro. 
A cewar wani mazaunin Adunu, John Lazarus, 'yan bindigan sun fara aikata wannan ɗanyen aikin ne da misalin ƙarfe 8:00 na safiyar ranar Talata. 
Ya ce tun daga wannan lokacin suka tsare mutanen ƙauyukan har zuwa ƙarfe 3:00 na rana. 
Mutumin ya kara da cewa da yawan mutane a Daji suka kwana tsawon daren nan saboda tsoron kar 'yan bindigan su sake kaddamar da wani harin idan sun koma gida. 
Sakamakon haka, Mista John Lazarus ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro a Najeriya su taimaka su kawo masu ɗauki. Lazarus ya yi ikirarin cewa yan ta'adda sun ƙara matsawa wajen kai hare-hare kan mutane a tsawon watanni uku na baya-bayan nan amma ga dukkan alamu gwamnati ba ta ɗaukar wani matakin a zo a gani.