'Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallacin Juma'a a Zamfara, Sun Sace Mutane Da Dama 

 'Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallacin Juma'a a Zamfara, Sun Sace Mutane Da Dama 

 

'Yan bindiga a ranar Juma'a sun sace masallata masu tarin yawa daga Masallacin Juma'a na yankin Zugu dake karamar hukumar Gummi ta jihar Zamfara, Mazauna yankin sun ce 'yan bindigan sun boye bidigoginsu a cikin kayansu kuma suka shiga masallacin yayin da liman yake dab da fara huduba, Daily Trust ta rahoto. 

Maharan sun sanar da wadanda ke wajen Masallacin da su shiga ciki. 
"A lokacin da suka zagaye masallacin, sun bukaci duk wadanda ke wajen masallacin da su shiga ciki cewa sun zo ne domin tattauna kan yadda zasu sako wasu mutanen dake hannunsu. 
"Babu wanda ya gansu da bindigogi kuma mutane da yawa sun kallesu a matsayin masu bauta. 
Babu wanda ya mayar da hankali kansu saboda sun boye bindigoginsu. "Sai dai, jim kafdan bayan sun shiga cikin masallacin suka fito da bindigoginsu tare da yin harbin gargadi. "Sun jagoranci masu bautar zuwa cikin daji amma wasu masu bautar sun yi nasarar arcewa daga masallacin. 
An sace Muezzin amma Liman ya sha da kyar," cewar wata majiya. 
Abubakar mazaunin yankin ya kara da cewa: "Wasu daga cikin wadanda ke wajen masallacin duk an yi garkuwa da su saboda basu san 'yan bindigan sun tsaya a wurare daban-daban a wajen masallacin ba. 
Sun yi harbe-harbe a iska sannan suka tarkata jama'a zuwa daji."
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, yace har yanzu bai samu rahoton farmakin ba amma ya yi alawakrin karin bayani idan ya samu daga bisani.