Yan bindiga sun Hana karatun Islamiyya a Katsina

Yan bindiga sun Hana karatun Islamiyya a Katsina

A  yammacin Assabar nan ne 'yan bindiga suka shiga garin Safana ta Jahar Katsina, inda suka shiga har cikin garin suka watse  mutane. 

Al'umma suka kama guje-guje don tsira da rayuwarsu. 
Sun harbi mutane sun tafi da wasu wanda har yanzun haka ba a kai ga tantance mutanen da suka tafi da su ba. Wani abin mamaki ma shi ne yanda suka dinga bin makarantun islamiyyar garin suna kora yara gidajensu.
Har yanzu ba wasu hukumomin tsaro da suka ce komai kan harin.