'Yan Bindiga Na Kara Samun Karfi A Arewa Maso Yammacin Najeriya

'Yan Bindiga Na Kara Samun Karfi A Arewa Maso Yammacin Najeriya
 

Daga Abbakar Aleeyu Anache.

 

Matsalolin rashin tsaro a Najeriya na cigaba da mamaye sassan kasar, suna ta illata yankunan arewa da jama'ar yankin.

 
Abinda ke nuna hakan shine yadda yan bindiga ke cigaba da fadada ayyukan su zuwa wasu sababbin yankuna da ba'a tunanin ayyukan su kai wurin kamar abinda ke faruwa yanzu a wasu yankuna na arewa maso yammacin Najeriya. 
 
A can baya akwai wasu yankunan Najeriya da suka yi kaurin suna akan ayyukan yan bindiga inda suka kafa sansannoni suna cin zarafin jama'a alal misali kamar yankin gabascin Sokoto dake arewa maso yammacin Najeriya.
 
Duk da yake har yanzu yan bindigar na cigaba da tafka ta'asar su a wasu daga cikin wadannan yankunan, haka ma suna fadada ayyukan zuwa wasu sababbin wurare. 
 
Yankin Durbawa dake cikin karamar hukumar kware wadda daga ita sai kwaryar birnin Sokoto ya soma daukar bakuncin yan fashin daji inda jama'ar garin suka soma kokawa.
 
Uban kasar yankin Mu'azu Yakubu Durbawa ya nuna damuwa akan idan ba'a yi saurin kawo daukin magance matsalar ba to fa ba'a san adadin illolin da zata haifar ba.
 
Sau da yawa jami'an tsaro ke cewa suna kan kokarin su na magance matsalolin da samar da tsaron rayukan jama'a amma kuma matsalolin na cigaba da wanzuwa abinda masharhanta kamar Farfesa Bello Baddah ke cewa da ana samun hadin kan mahukunta ga tunkarar wannan matsalar tamkar yadda suke hada kai a fage siyasa da watakila zuwa yanzu matsalar ta zama tarihi. 
 
Yan Najeriya dai na cike da fatar ganin lokacin da za'a samu fita daga wadannan musifu ko da talaka zai samu saukin rayuwa.