'Yan bindiga ke noma gonakinmu a jihar Neja---Mutanen jiha

'Yan bindiga ke noma gonakinmu a jihar Neja---Mutanen jiha

Rahotanni daga jihar Neja na cewa a yanzu haka ƴan bindiga da dama na zaune a cikin gidajen al’ummar garin Allawa , kuma su na noma a gonakinsu tare da yin anfani da takin zamanin da su ka bari a gidajensu.

Watanni biyar kenan da su ka gabata ƴan bindigar su ka fattataki mazauna garin na Allawa tare da korar su daga matsuguninsu kuma su ka mayar da su ƴan gudun hijira.

Wani mazaunin garin wanda ke gudun hijira ya shaida wa BBC cewa,lamarin ya faru ne bayan da gwamnati ta janye jami'an tsaron da ke basu kariya domin a cewar gwamnatin tana so ta canza tsari, "sai dai har yanzu ba a mayar da sojojin ba."

"Wasu daga cikin mu sun yi ƙundinbala, kasancewar halin matsi, sun yi ƙoƙarin leƙawa domin su gani shin gari na komowa, sai dai sun iske abun mamaki, an ƙoƙƙona gidajenmu, sun kuma  takin da muka baro suna amfani da shi a yankin Allawa, yanzu haka ɓarajin suna noma a dajin Allawa." 

Mutumin da muka sakaya sunansa, ya ce ba su taɓa tunanin haka za ta faru ba, "kasancewar gwamnati, ta yi mana alƙawarin za ta yi abun da yakamata, amman har yanzu ba ta yi abun da yadace ba.

Ya kuma shaida wa BBC cewa suna fatan sake komawa garin na su, "maganar komawa akwaita, in har gwamnati za ta tallafa mana."

Sai dai gwamnatin jihar Neja ta musanta wannan iƙirari na zaman ƴanbindiga cikin garin Allawa.

Kwamishinan tsaro na jihar Neja, Bello Muhammad ya ce gaskiya ne mutanen ba sa gidajensu, sai dai ba gaskiya bane cewa ƴan bindiga suna gidajensu suna kuma noma a wajen.

"Idan suna noma a wajen ai kamasu za mu je mu yi, koda sojoji ba su wurin amman ana rangadi har ta sama kowane lokaci, bamu da sansanin ƴanbindiga a jihar mu," cewar kwamishina.

Gwamnatin ta jihar Neja ta ce tana nema wa mutanen wurin da za su koma domin su ci gaba da yin rayuwa tare da yin noma a wasu wuraren.