'Yan Bindiga Cikin Shigar Mata  Sun Sace Mutane Masu Yawa a  Zamfara 

'Yan Bindiga Cikin Shigar Mata  Sun Sace Mutane Masu Yawa a  Zamfara 

 

'Yan bindiga sun ɓadda kama cikin shigar mata sun kai farmaki a ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da mutane masu yawa. 

A cewar rahoton Daily Trust, mazauna garin sun bayyana cewa 'yan bindigan sun kawo farmakin ne da misalin ƙarfe 7:00 na yamma a ranar Litinin, 14 ga watan Agusta. 
'Yan bindigan waɗanda suka zo a kan babura sun kama harbi kan mai uwa da wabi kafin daga bisani suka tasa ƙeyar mutane masu yawa ciki har da mata da ƙananan yara.
Garin da ƴan bindigan suka farmaka bai wuce tafiyar kilomita 30 ba zuwa ƙaramar hukumar Bungudu inda a ranar Lahadi ƴan bindigan suka sace mutum bakwai ciki har da ɗan sarki.
Wani majiya a garin ya bayyana cewa,  "Ƴan bindigan sun farmaki garin ne ana gama Sallar Maghriba inda suka kama harbe-harbe. Mutane sun riƙa guduwa domin neman tsira inda ƴan bindigan suka riƙa bin su har cikin gidajensu suna tafiya da su." 
"Duk da cewa ba a san adadin yawan mutanen da aka sace ba, ƴan bindigan sun tasa ƙeyar aƙalla mutum 50." 
Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan Jihar Zamfara, CSP Muhammad Shehu, ya ci tura domin bai ɗauki kiran da aka yi masa a waya ba, sannan bai dawo da amsa ba kan saƙon da aka tura masa ta waya har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.