Home Labarai Yaki Ya Barke, Israila Ta kai Hari Kasar Iran, An Ji Fashe...

Yaki Ya Barke, Israila Ta kai Hari Kasar Iran, An Ji Fashe Fashe a Tehran

6
0

Rahotanni sun nuna cewa kasar Yahudawa ta Isra’ila ta kaddamar da hare-hare kan Iran da safiyar Asabar, 28 ga Fabrairun 2026. 

Hakan na zuwa ne bayan gaza cimma matsaya tsakanin Iran da Amurka a wata tattaunawa da suka yi a kasar Oman game da wasu abubuwa. 

Rahoton tashar Aljazeera ya nuna cewa a halin yanzu, babu wata sanarwa ta hukuma daga Iran game da harin da aka kai musu. Hankula sun koma kan jin martanin da Iran za ta yi, da abin da Amurka za ta ce kasancewar ta sha alwashin kai hari kasar a baya. 

A bisa rahotannin da aka samu, an sanya asibitocin Iran cikin shirin ko-ta-kwana, an kuma tura motocin daukar marasa lafiya a wurare.

Mai magana da yawun ma’aikatar Lafiya ta Iran ya ce an sanya asibitoci cikin shirin ko-ta-kwana ne domin samun damar kula da wadanda za su iya samun rauni.

 An samu karin bayani daga shugaban kwamitin tsaron kasa na Majalisar dokokin Iran, Ebrahim Azizi game da harin, inda ya ce: “Mun gargade ku!” “Yanzu kun shiga wata hanya da karshenta ba ya hannunku,” 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here