Yadda Za Ki  Samar Da Garin Sakwara Cikin Sauƙi

Ina uwar gida da Amarya, harma da 'yan mata? Ku zo ku ji....

Yadda Za Ki  Samar Da Garin Sakwara Cikin Sauƙi
 
Daga Maryam Ibrahim (DOCTOR MARYAMAH).
 
 
Ina uwar gida da Amarya, harma da 'yan mata? Ku zo ku ji....
 
Da farko idan maigida ya siyo doya, kuma kina gudun ta lalace ba'a amfana da'ita ba. Kina iya yankata daidai yadda ki ke ra'ayin ta. Ki nemi tafasasshen ruwan zafi ki saka wannan doyar da ki ka yayyanke a ciki. Bayan kamar minti goma sai ki tsame ta. Ki shanya ta bushe ta yadda zaki mayar da'ita gari. Idan ta bushe zaki iya dakawa a hannunki, ko kuma ki kai a engine a markaɗe mi ki ita.
 
Zaki dinga ɗibar garin kina tuƙawa yadda ki keyin tuwo haka za kiyi. Za ki ga yadda sakwararki za ta yi gwanin kyau, sai ma ansa a baki za'a fahimci kyaun na musamman.