Yadda Za Ki Haɗa MANGO JUICES Mai Daɗin Gaske
MANGO JUICES
_Abgkyari's kitchen_
Mangoro babba 1
Lemon tsami 1
Sugar
Kanamfari 4
Star anise 1
Da farko ki wanke mangoron ki da lemon tsamin ki,
Ki yanka mangoro ɗin, ki cire naman cikin sa tass, ki bar fatar.
Sannan kizuba a blender, ki matsa mishi lemon acikin,
Ki zuba ruwa ki markaɗe shi.
Bayan kin markaɗe,sai ki qara ruwa ki tace shi,
Ki dauki iya adadin sugar da kikeso ki zuba a tukunya sai ki zuba kanamfarin da Star anise ɗin,
Ki dafa su na minti 5,
Shikenan ki sauke ki juye akan mangoronki da kika tace,
Ki gauraya su tsaf, sannan ki zuba a mazubinki,
Kisa a fridge ko ki sa qanqara kisha abinki.
Angama juice ɗin mangoro.
❗ba dole bane dafa sugar,amma yafi dad'i.
❗Kisa ruwa iya kaurin da kikeso.amma idan kika zuga ruwan taste ɗin mangoron zai fita.
❗Lemon tsami yana hana shi ɓaci da wuri,sannan yana bashi ɗan ɗano mai daɗi abaki.
❗Ban cire kanamfarin da Star anise ɗin ba, haka na zuba a mazubina.
Idan bakyason su ki cire su.
Abgkyari's kitchen_