Yadda Za Ki Haɗa Kunnun Aya Na Musamman

Yadda Za Ki Haɗa Kunnun Aya Na Musamman

ZEZA'S CUISINE


Yadda Za Ki Haɗa Kunnun Aya Na Musamman


Kayan Hadi

* Aya
* Kwakwa
* Dabino 
* Sugar
* Madara 
* Flavor

Yadda Za Ki Hada Kunun

Ki gyara ayarki ki cire duwatsu da dattin cikin sannan ki jika a ruwa ya yini ko ya kwana amma idan zai kwana ki tabbata cin canza ruwan gudun kada ta yi tsami, sannan ki cire kwallon cikin dabino ta jika dabinon, ki yayyanka kwakwarki kanana, idan kin zo markada wa sai ki zuba wanke ayar ki zuba a blender, ki zuba kwakwa da dabino a kai kiyi blending ko ki kai inji a markado miki ita, bayan kin markada sai ki tace da kyalle akalla sau biyu, sannan ki zuba sukari da flavor da kankara, idan anzo sha kuma sai a zuba madara ta ruwa ko ta gari.
Shi kunun aya baya son zafi da zaran yayi zafi to zata yi yauki, sai a bar ta a kankara ko a saka ta a frizer….

chief zeza