Jami'an kamfanin wutar lantarki na Kaduna sun dandana kudarsu lokacin da sojoji suka farmaki kamfanin da ke jihar Kebbi inda suka yi wa ma'aikatan da ke bakin aiki dukan tsiya.
An tattaro cewa sojoji sun farmaki kamfanin ne a ranar Asabar kan zargin yanke wutar lantarki da ke sansanin sojoji na Dukku da ke Birnin Kebbi, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Da yake watsi da lamarin, shugaban sashin sadarwa na kamfanin lantarkin Kaduna, Abdulazeez Abdullahi, ya ce sojojin basu taba kai korafi dangane da aikinsu ba kafin suka farmaki ma'aikatansu.
"A zahirin gaskiya, yunkurin da tawagarmu a jihar Kebbi suka yi inda suka bukaci ganawa da rundunar sojin don tattauna batutuwa ya ci tura.
"Dakarun sojojin sun farmaki harabarmu a ranar Asabar sannan suka farmaki wasu ma'aikata da kwastamomi. "Sojojin sun yi wa mutanen mugun duka tare da cin mutunci ba tare da dalili ba.
wannan ta'asar bai da gurbi a al'ummar da muke ciki. "Muna burin fitowa fili mu ce kamfanin lantarkin Kaduna ba zai ba da tabbacin aikinsa ba saboda rashin tsaro. Lafiyar ma'aikatanmu na da matukar muhimmanci.
"Bama yarda da irin wannan tsoratarwa da cin zarafin ma'aikatanmu kuma za mu dauki matakin da ya dace da doka don neman gyara."
"Duba ga lamarin tsaron a kasar nan, musamman a yankin arewa, ya kamata KAEDCO ta yi taka-tsan-tsan wajen katse duk wata kafa na sojoji.
"Barin sansanin sojoji kamar sansanin Dukku, inda ake ajiye manyan makamai cikin duhu yana da matukar hatsari."