Daga Muhammad Umar Faruk.
Masu iya magana kan ce "labari yafi dadi daga bakin mai shi" Dr Yakubu Moddibo (Yakubu M Kumo). ya karkato da akala da kuma hankali da alumar duniya baki daya zuwa ga halayya, mu'amala, al'adu da kuma addinin malam Bahaushe, da manhangar Hausawa mazauna Arewa a zahiri, ba kamar yanda aka saba shati fadi ba.
Idan fim yayi kyau mafi akasari jarumai da masu bada umarni ake yabawa, so da yawa mutane suna manta muhimmancin marubucin labarin fim din shi kansa, wanda in babu shi fim din ba zai samu asali ba. koda yake, dukkanin su nada hannu a irin wannan al'amari.
Kamar hoto ne ne, idan mutane suka ga hoto yayi kyau za su yi murna da kuma farin chikin ganin wannan hoto saboda ya yi kyau, amma mafi akasari a bama tuna wanda ya dauki wannan hoton, wanda da ba don jajircewa da kuma kokarin shi ba, da ba za mu ga hoton ba.
Marubuci dai shi ne wanda yake aiki da ilimi, baiwa da kuma fasahar da Allah ya bashi wajen kirkiran labari, jeranta, kawata da kuma baiwa shi kansa labarin sifar da har zai gamsar da masu kallo.
Marubuci Yakubu M Kumo an haifeshi ne a jihar Gombe, ya kasance marubucin da ya rubuta labari na fim akalla 200 daga shekarar 2009 zuwa yanzu a kiyasi, ya shirya finafinnai shida a Kannywood a Karkashin kamfanin sa Mai suna(Kumo production).
Sannan ya Sami lambar girmamawa a masana'antar matsayin Wanda yafi tsara labarai tsakanin shekarar 2014 zuwa 2016, a kwanakin nan kuma ya samo shedar karramawa ta 'pandora Award' yayi karatunsa na Furamare da Sokandare a Gombe, sai ya tafi jami'ar Bayero ta Kano.
Abun da zai burge mutane shi ne Dakta Yakubu M. Kumo, yana da 'Phd' a fannin 'Islamic Studies', kuma malami ne a jami'ar Gombe mallakar jiha(GSU).
Akowane lokaci da Mai kallo zai gamsu da fim kan kokarin jarumai da kuma fasahar masu shiryawa, ya kamata mu tuna cewa asalin ginshinkin kowane fim shi ne labari, kuma labari ana samun shi ne daga marubuci, ko kuma marubuta.
A yanzu masu kallon finafinnan Hausa sun zarce yanda ake tunani, hakan ya faru ne a sanadin gyara da sauye-sauye wurin rubutun zamani, da kuma aiki na'urori na zamani da ake yi a masana'antar, mutanen arewa sun farka cewa finafinan Hausan nan dai suna da fa'idoji da dama, kuma suna bada gagarumin gudumawa wurin fadakarwa, fannin zamantakewa, addini da kuma al'adun Malam Bahaushe.
A yanzu finafinnan da Hausawa suke shiryawa suna jan ra'ayin masu kallo duba da yanda suke zagaye duniya suna kuma fafatawa wurin shiga lungu lungu da sako sako da ko wane irin fim zaya iya kaiwa, a yanzu haka fim din Hausa ya fara shiga kafa ta yada finafinnai a Duniya wato 'Netflix', duk duniya kowa zai iya kalla, ba sai Bahaushe ko kuma mai jin yaren Hausa ba.
Dakta Yakubu M. Kumo yana da mata da 'ya'ya. Shi mai rubutu ne, kuma a wani lokaci mai shiryawa a masana'antar fim ta Hausa, ana masa shaida mai kyau gurin sanin ya kamata, kamun kai, kyakyawar mu'amala da mutane, addini da kuma rikon amana.
Wasu daga cikin finafinan da ya rubuta sun hada "Abbana, Cikin waye, Daga Allah ne, Hanyar Kano, Makaryaci.
"Manyan Mata, Mati a Zazzau, Kishiyata, Labarina(wanda a kwana kin nan ya samu masu kallo sama da mutum miliyan daya cikin awa 24)" abun da ya zamo na fari a tarihin Kannywood baki daya. Finafinan da ya rabuta sun yi fice a kowane gida a arewacin Nijeriya.
Akwai masu rubutu da daama a masana'antar ama Dakta Yakubu yayi fice duba da yadda yake kokari matuka gurin rubuta labari mai ma'ana, a koda yaushe, kuma ana yawan ganin tasirin ilimin addini a cikin rubutun nashi.
Darasi: Baiwa daga Allah da yake, kuma kowa da irin baiwar da Allah ya bashi. yanada kyau mutane kar su raina baiwar da Allah ya bawa wannin su, kuma ya kamata mu dinga bada karfin guiwa wurin tallafawa masu sha'awar wakoki, wasan kwaikwayo, da kuma rubutu, damin su ma su girma har su iya bada nasu gudumawar daga irin baiwar da Allah ya ba su.
Muhammad Umar Faruk haifeffen garin gombe ne, jarumi me sha'awan wasan kwaikwayo, marubuci, kuma shugaban kasuwanci da hada hada a companion jaridar 'North East Times Papers'.