Mutanen Sakkkwato sun fara tuuruwa domin sayen kayan Sallah a babbar kasuwar Sakkkwato duk da matsin tattalin arziki da ake fama da shi ga jama’a.
Wakilinmu ya ziyarci kasuwar in da mutane ke ta hada hada musamman a wuraren da ake sayar da takalma da huluna da kayan kwalliya na mata da sauran kayan sa ake bukata domin kwalliyar sallah.
Sabira Muhammad wata Mata ce da ta zo sayen hula ga yaranta maza su biyar ta ce gaskiya kayan akwai tsada sosai da kyar aka barmin kowace hula daya kan farashi dubu 23 a haka na saya domin yaran su yi kwalliyar sallah.
“Matsin tattalin arziki yana wahalar da mu sosai kudi a yanzu ba su da daraja sai ka samu kudi masu yawa amma abin saye kadan a hula kawai na kashewa yarana sama da dubu 100, saura takalma da kayan kwalliya na mata ka ga abin ya yi yawa ina ga sutura Kuma don Zan sayawa Mata jallabiya don ita suke son sanyawa a ranar Sallah,” in ji ta.
Malami Muhammad da ya je sayawa Kansa da dansa takalma ya ce kayan a yanzu suna da tsada in har za ka sayi takalma masu dama daga dubu 15 suke farawa.
“Na sayawa yarona takalma na dubu 18 ni kuma na sayi na 15,000, sabanin baya da wannnan ba za su wuce dubu 10 ba,” a cewarsa.
Haka za ka samu kowa yana sayen abin baifi karfinsa ba, ana sayen ana komawa ba yanda za a yi dole a saya tun da bukatun rayuwa ne.






