Yadda Ake Fish Balls A Cikin Sauƙi
BASAKKWACE'Z KITCHEN
Yadda Ake Fish Balls A Cikin Sauƙi
INGREDIENTS:
Ice fish,
Eggs
Tattasai,
Tarugu,
Albasa
Curry,
Thyme,
Citta,
Tafarnuwa,
Kanunfari
Maggi
Gishiri,
Oil
Kayan ƴamshi
PROCEDURE
Da farko Ki sami ice fish masu kyau, sai ka wanke tafasa, bayan ya tafasu sai ki sauke ki barshi ya huce, sai ki cire dukkanin tsokar a kwano. Sai ki farfasa shi shi sosai. Sannan ki daka tattasai, tarugu, da tafarnuwa su daku sosai. Sai ki zuba a kan kifin, sai ki ɗauko ragowar albasan ki yanka shi ƙanana a kan kifin, kisa citta kaɗan, kisa curry, gishiri, thyme, dama sauran su.
Sai ki jujjuya su haɗe, daga nan sai ki rinƙa dunkula su kamar yadda hoton ya nuna, sai ki sami ƙwai ki kaɗa a kwano, kisa maggi kaɗan da gishiri, sai kisa mai a wuta yayi zafi. Sai ki rinƙa ƙauko dunƙulallen kifin nan kina tsomawa a ƙwai kina sawa a wuta yana soyuwa, amma kada ki cika wuta, saboda kada ƙwan ya soyu har yayi baki amma kifin bai soyu ba.
MRSBASAKKWACE
managarciya