Home Manyan Labaru Ya rasa ransa ƙoƙarin ceto Akuya cikin rijiya a Oyo

Ya rasa ransa ƙoƙarin ceto Akuya cikin rijiya a Oyo

2
0

Hukumar kashe gobara ta Jihar Oyo ta ciro gawar wani mutum mai shekara 45 da ya rasu a cikin wata rijiya mai zurfi, yayin da yake ƙoƙarin ceto wata akuya da ta faɗa rijiya a yankin Mokola da ke cikin kauyen Saki.

Shugaban hukumar, Mista Moroof Akinwande, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Ibadan.

Ya ce, “Mun samu kiran gaggawa kan wannan lamari ne a ranar Litinin da misalin ƙarfe 10:23 na dare, ta wayar tarho daga wani mai suna Yusuf Ismail.”

A cewarsa, jami’an hukumar ƙarƙashin jagorancin Pfs II Kolade Taiwo sun garzaya wajen da lamarin ya faru ba tare da ɓata lokaci ba.

Da isarsu wurin, sun tarar da wani mutum mai shekara 45 da ya makale a cikin rijiya mai zurfi.

“Jami’anmu sun ɗauki mataki cikin gaggawa, suka ɗaure shi da kayan aikin da suka dace, aka gudanar da aikin ceto, inda aka ciro gawar mutumin daga cikin rijiyar,” in ji shi.

Shugaban ya ce lamarin ya faru ne lokacin da mutumin ya shiga rijiyar da nufin ceto akuya da ta faɗa ciki ta kasa fita.

Akinwande ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, tare da gargaɗin jama’a da su guji shiga rijiyoyi saboda haɗarin da ke tattare da hakan, yana mai cewa hakan na iya haifar da rauni ko ma mutuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here