An kama wani mutum a Yobe bisa zargin kashe wani mutum saboda zargin soyayya da matarsa
Rundunar ’yansandan Jihar Yobe ta kama wani mutum mai shekaru 50, Alhaji Hassan Umaru, bisa zargin kashe wani ɗan kauyensu mai shekaru 45, Sukari Abdul, sakamakon zargin yana da alaƙar soyayya da matarsa.
A cewar kakakin rundunar, SP Dungus Abdulkarim, lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 1 ga Fabrairu, 2026, da misalin ƙarfe 12:30 na rana, a ƙauyen Bundila da ke ƙaramar hukumar Gulani ta jihar. Rahotanni sun nuna cewa rigimar ta barke ne a kasuwa, inda ake zargin Umaru ya kai wa Abdul hari da adda.
An garzaya da wanda abin ya shafa zuwa Cibiyar Kula da Lafiya ta l ta Bularaba, inda likita ya tabbatar da rasuwarsa. Hukumomi sun ce an kama wanda ake zargi nan take, tare da ƙwato makamin da aka yi amfani da shi wajen kai harin.
An mika shari’ar zuwa sashen binciken manyan laifuka na Jiha (CID) domin gudanar da cikakken bincike.
Da yake mayar da martani kan lamarin, Kwamishinan ’yansanda, CP Emmanuel Ado, ya shawarci al’umma da kada su ɗauki doka a hannunsu, musamman a rikice-rikicen aure ko na zamantakewa, tare da kiran jama’a da su rika kai koke-kokensu ga hukumomin da suka dace.






