Wuta ta ja ɓarawon waya a jikin taransifoma ya mutu a Damaturu
Wuta ta ja wani da ake zargin ɓarawon waya ne a lokacin da ya ke kokarin sace wata wayar wuta da take tsirara kuma da wuta a jikin a jikin wata taransifoma a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.
Blessing Tunoh, jami’ar yaɗa labarai ta Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Yola, YEDC, ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a Yola a yau Asabar.
Madam Tunoh ta ce Manajan Shiyya na kamfanin, ɓangaren aiyuka, ya ziyarci wurin tare da jami'in, bayan samun rahoton faruwar lamarin.
Ta ce, tawagar ‘yan sandan da ke sintiri a Damaturu ne suka fitar da gawar wanda ake zargin daga tashar jikin taransifoma din sannan kaanjwj zuwa Asibitin Koyarwa na Damaturu.
Kakakin kamfanin ta ce ‘yan uwan mamacin sun zo sun gano gawar marigayin a lokacin da aka isa da shj asibiti kuma suka karbe shi.
“Bincike ya nuna cewa marigayin ya yi yunkurin yin amfani da rigarsa wajen kare kansa a lokacin da yake kokarin cire wayar é da wata wayar da aka fallasa a lokacin da ya aikata wannan aika-aika.
Sai dai abin takaici, mu’amala da na’urar kai tsaye ta kai shi ga wuta nan take amma na’urar taranfoma ba ta lalace ba, kuma ba a sake samun wata barna ba,” inji ta.