Wike Ya Tada Hankalin Jama'a Ya Fadi Wadanda Zai Sa Kafar Wando Daya Da Su

Wike Ya Tada Hankalin Jama'a Ya Fadi Wadanda Zai Sa Kafar Wando Daya Da Su

 

Jim kadan bayan rantsar da shi a matsayin ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya tada hankalin jama’a da ya fadi manufofinsa. 

Da yake zantawa da jama’a da manema labarai a ma’aikatarsa, AIT ta rahoto mai girma ministan ya na bayanin yadda zai dawo da martabar birnin Abuja.
Nyesom Wike ya yi alkawari Abuja zai shiga cikin biranen da ake ji da su a duniya, amma da alama dole a kawo matakan da mutane za su koka da su.
"Za mu tattauna da masu ruwa da tsaki da sauran jama’a, da masu kiwo. Dole a daina ganin shanu a Abuja, ba za mu kyale shanu na yawo cikin birni ba. 
Za su iya yin kiwonsu a wajen gari amma ba birni ba. An shuka ciyayin nan ne domin kawata birnin, ba irin ciyawar da dabbobi za su rika ci kenan ba." 
Tashar ta rahoto tsohon gwamnan ya na cewa za su tatauna da makiyaya, domin ya na da muhimmanci a daina cin karo da tumaki a hanyar Aso Rock. 
Har ila yau, sabon ministan ba zai bari kasuwanni su cika ko ina kaca-kaca ba, ya ce ba za ta yiwu ba. "Ko ina kasuwa ne, ba za mu lamunta ba. Na san abubuwa sun yi wahala, amma bai nufin a takurawa al’umma, dole neman abinci ya zama a kan doka.
Ba za a ce mutane su na wahala, saboda haka ko ina ya zama kasuwa ba. Ba za mu yarda da wannan ba. Mutane su na saida kaya karkashin lema a birni." 
A cewar Wike, hakan ya na jawo rashin tsaro kamar yadda ake barin kango ba a karasa ginawa ba. 
Punch ta rahoto jigon na PDP ya na cewa zai fatattaki masu babur da keke napep, a cewarsa masu hayar na kawo cinkoso bayan jefa rayuka a hadari. Wadanda su ka bar gidajensu su zama mafakar marasa gaskiya za mu karbe su. Ka yi shekaru 15 ka na gina gida.
Kango ya zama wurin marasa gaskiya. Gwamnati za ta karbe gidajen nan musamman Maitama, Asokoro da Wuse, duk zan karbe.