Wike da magoya bayansa sun gabatar da sharudda kafin amincewa da babban taron PDP
Shugabannin jam’iyyar PDP masu goyon bayan Ministan Abuja, Nyesom Wike, sun gindaya sharudda kafin gudanar da taron gangamin kasa na jam’iyyar.
A taron da suka gudanar a Abuja karkashin ƙungiyar Eminent Leaders and Concerned Stakeholders of PDP, sun dage cewa Shugaban PDP na ƙasa ya ci gaba da kasancewa daga Arewa ta Tsakiya, kamar yadda aka tsara a rabon mukaman taron 2021.
Haka kuma sun bukaci a gudanar da sabbin tarurruka a jihohin Ebonyi da Anambra, da taron kananan hukumomi a Jihar Ekiti, tare da sake kiran sabon taron yankin Kudu maso Gabas.
Sun kuma nemi a mutunta sakamakon taron Kudu maso Kudu da aka yi a Calabar, wanda kotu ta tabbatar da sahihancinsa.
Tsohon gwamnan Benue, Samuel Ortom, wanda ya karanta sanarwar bayan taron, ya gargadi cewa rashin bin wadannan sharudda zai sa kowanne taron gangami da aka yi ya zama babu inganci, domin sahihan mambobin jam’iyya za su rasa damar shiga.
Taron ya samu halartar Wike, wasu tsoffin gwamnonin jihohi, ‘yan majalisar kasa na yanzu da na baya, da shugabannin PDP daga jihohi da dama.
Shugabannin sun jaddada cewa PDP dole ta tsaya kan adalci, gaskiya da bin doka idan har tana son dawowa matsayin jagorar adawa a Najeriya.
managarciya