WHO ta shirya wa 'Yan Jarida taron karawa juna sani na kwanaki uku a Yobe

WHO ta shirya wa 'Yan Jarida taron karawa juna sani na kwanaki uku a Yobe

 

Daga Muhammad Maitela, Damaturu.

 

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) da hadin gwiwa da Ma'aikatar lafiya ta jihar Yobe, a ranar Laraba sun shirya taron karawa juna sani na kwanaki uku, ga Yan Jarida hadi da masu hulda da Kafafen sada zumunta (Social Media Influencers) domin samun horo wajen bayar da sahihan rahotanni kan barkewar annobar cutuka masu saurin yaduwa.

 
Taron bayar da horon ya na gudana ne a babban dakin taro dake 'Sand Dune Hotel' a Damaturu, babban birnin jihar Yobe; wanda ya samu halartar Yan Jarida da masu hulda da kafafen sada zumunta daga kowane bangaren jihar.
 
Da yake jawabi a wajen taron, Ko'odinatan Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a jihar Yobe, Dr. Ningi Barau ya bayyana cewa, makasudin shirya horon shi ne domin karkato da tunanin jama'a zuwa samun sauyin dabi'u dangane burin da ake dashi a fannin bunkasa harkokin kiwon lafiyar al'umma a jihar Yobe.
 
Dr. Ningi ya kara da cewa, muhimmancin yada labaru tare da sahihan bayanai abu ne mai matikar alfanu wajen dakile kowace barazana ta bazuwar annobar cutuka masu saurin yaduwa idan sun barke.
 
“Saboda idan ba a wayar da kan jama'a ba dangane da irin wadannan cutukan ba; musamman yadda ake kamuwa dasu, ko kuma yanayin cutukan, da matakan da ya dace su dauka idan sun kamu, ka ga kenan akwai dimbin matsaloli."
 
"Saboda zai yuwu mutane su harbu da cuta ba tare da sun sani ba, alhalin ita kuma cutar zata yi ta bazuwa, ta fantsama cikin mutane bila adadin, al'amarin da ka iya kaiwa ga rasa rayuka da dama." In ji Ko'odinatan WHO na Yobe.
 
Sa'ilin da yake karin haske dangane da makasudin shirya horon, daya daga cikin ma'aikatan hukumar WHO, Mr Kingsley Igwebuike, ya jaddada cewa taron zai taimaka wajen bunkasa ilimin mahalartan ba a fannin bayar da rahotanni kadai ba.