WATA UNGUWA:Fita Ta Huɗu
A taƙaice dai kwanansu uku a Asibiti ba tare da Mudi ya leƙa su ba, a wuni na huɗun ne da yamma Lis Inna ta tattaro ƴaƴanta suka gudo daga Asibitin sakamakon ba su da kuɗin da za su siye magani, shi ne likitoci suka bar su nan a yashe, gashi har lokacin Mudi bai leƙa su ba acewarsa "Duk tsuntsun da ya ja ruwa ai shi ruwa kan doka." Cike da jin haushin wulaƙancin da aka masu ta yo gida da su.
P 4
BABI NA HUƊU
Cikin hanzari Maryam ta yi kan Hanifa girgizata ta shiga yi tana faɗar "Yaya Hanee don Allah ki tashi." Shiru ta ji kuma ba alamun motsi a jikin Hanee, hakan ya ƙara dugunzuma hankalinta.
Kamar wacce aka tsikara da tsinke ta zabura ta yi kan Sofi domin ta yanke ƙauna da samun rayuwar Hanee.
Nan ma hawa jijjiga jikin Sofin ta yi. "Yaya Sofi tashi, ki tashi."
Nan ma ta ji shiru "wayyo Allah na na shiga uku ni Maryam kenan mutuwar kasko kuka yi?"
Ihu ta ratsa sai ga hawaye sun ɓalle a idonta tamkar famfo, da tasan tashin hankalin da zata zo ta riska kenan da bata tafi aiken ba ko meye zai faru da ita kuwa.
"Sadik je ka kira Baba ƙarami(ƙanin Babansu)" da gudu yaron ya fice Basma na take masa baya domin su ma sun firgita ainun, duk da cewa su yaya Mankas sau tari suna ɗebo rigima har a raunata su, amma dai ba a taɓa yi agabansu ba sai dai su ga rauni.
Bayan fitar su Maryam ta kasa jure kallon 'yan'uwan nata da jikinsu ke zubar da jini, Ba ma kamar Hanee da aka fasawa gefen ciki. Ta rasa abinda zata yi, hankalinta ya kai linta gurin tashi, ficewa ta yi daga gidan cikin hanzari ta shiga gidan Malam Hadi don ta kirawo shi, gani take duk bata lokaci ne ta tsaya jiran zuwan Baba ƙarami.
Can bayan minti biyar suka shigo gidan tare da Malam Hadi, da ya ga abinda ke faruwa ya shiga damuwa Sosai ganin yanda 'yan'uwan biyu suka raunata junansu sakamakon biyewa son zuciya 'yan magana sun yi gaskiya da suka ce 'zuciya mugun nama.'
Sai da ya gama tantance yanayin da suke ciki ya ɗago tare da cewa "Ki kwantar da hankalinki Maryama, na fi tunanin doguwar suma suka yi ba dai mutuwa ba, bari na taro abun hawa sai ki nemo waɗanda zasu kama mana a fitar da su."
Rufe bakinsa ke da wuya sai ga Baba ƙarami ya shigo har yana haɗawa da gudu, sallama bata ko samu ba, tsabar ɗimaucewa da ya yi domin shi a yanda Sadik ya gaya mishi wai sun kashe kansu ne.
Nan dai malam Hadi ya kwantar masa da hankali, sannan suka fitar da 'yanmatan zuwa titi, domin su ma Napep bata shigowa layinsu.
Ba iya layinsu ba, kusan duk rabin layukan unguwar hakane saboda matsatsinsu.
Asibiti gwamnati suka nufa da su domin a basu taimakon gaggawa.
Duk wannan bidirin da ake Baba bai Sani ba don kuwa bai dawo ba sai ƙarfe shida na yamma a nan ya tarar ba kowa, har ƙananun yaran sun fice zuwa maƙwafta domin neman abinda za su sakawa cikinsu.
Tabarma ya ɗauko ya Shimfiɗa a tsakar gidan yana cika da batsewa, ba haushin matar gidan yake ji ba, yaran gidan ne suka hassala shi, to gidan Ubanwa suka je suka bar masa ƙofar gida a buɗe.
"Amma yaran nan kwata-kwata basu da hankali, dubi yanda suka bar mun ƙofar gida a buɗe Salon a shigo a mana sata." Ya faɗa cikin bambami
Idan ka ji yanda ya haƙiƙice sai ka rantse da Allah yana da wani abun arziƙi da za a ɗauka a gidan, alhali ko Ɓeran Masallaci ya shafa masa lafiya akan tsiya.
A can asibiti abun Duniya ya ishi Baba ƙarami, jini ake nema za'a yiwa Hanifa ƙari domin ita ce ta yi asarar jini mai yawa, gashi kuma banda ɗari ukun da ke aljihunsa bai da ko ficika tare da shi.
Ƙarin damuwarsa shi ne tun bayan da suka samu ganin likita Malam Hadi ya fice kuma ya gaya masa ba gida ya nufa ba.
Babban abun takaicin daga Inna har Baba ba wanda ke da ko cover bare waya sukutum.
Yanzu kenan taya zan sanar da su Halin da ake ciki?
Can wata dabara ta faɗo masa a take ya aiwatar da ita ba tare da ya musawa ƙwaƙwalwarsa data haska masa tunanin ba.
A can gida kuwa matar Baba ƙarami ce ta shigo gidan Malam Mudi bayan sallar Magriba, zaune ta same shi yana ta bambami shi kaɗai kamar hauka sabon kamu.
"Yaran nan sun gama raina ni fa. Bari su dawo yau zasu ci na jaki a gidan nan, ni da kaina zan sadaukar da sauran jarumtata don na nuna masu shayi ruwa ne."
Assalamu alaikum." Ladi(matar Baba ƙarami) ta shigo gidan da sallamarta.
Amsa sallamar ya yi yana Faɗar "waye ne? shigo" ya fada kasancewar ba wutar lantarki hakan yasa ya gagara tuna sababbiyar fuskarta da yi sabo da ita.
"Sannu da hutawa Malam Mudi."
"Miƙewa ya yi yana Faɗar yawwa sannu." Sannan ya fara matsowa inda take da fitilar hannu riƙe a hannunsa yana haskawa a ƙoƙarinsa na son gano mai shigowar.
Murmushi ta yi ta girgiza kai "Malam Mudi Ladi ce, ina matar gidan? Ina tafe da muhimmin saƙo."
Ɗan murmushi ya yi "A'ah to,toh yanzu na ɗau haske ashe kece, wallahi bata dawo daga ƙauye ba tun saf......."
Kafin ya dasawa kalaminsa aya suka jiyo sallamarta daga waje alamun tana shigowa ne.
Hakan ya yi dai-dai da lokacin da aka dawo da wutar lantarki a take haske ya mamaye tsakar gidan.
"Shi ke nan ma, Hutaroro waken gizo ya ƙi yaya. Ga ta nan ma ta ƙaraso."
Shigowa ta yi bayan sun gama gaisawa da Ladi, Ladi ta ce "Dama abinda ke tafe da ni, Baba ƙarami ne ya ce in yi hanzari in zo in gaya maku cewa Hanifa da Safiya suna Asibiti sakamakon raunata junansu da suka yi garin faɗa."
"Inna dake ƙoƙarin zama ta yi Zumbur tare da juyowa waɗanne Hanifa da Safiyan ba dai nawa ba?"
"Luba kenan! Muna da wasu yaran ne masu irin sunan a zuri'armu?"
Juyawa ta yi ga Baba wanda shi ko akwalar rigarsa, hankalinsa kwance kamar tsumma a randa ta ce "Sai ka yi ƙoƙari ka ƙarasa asibitin nan ta baya, suna can tun yamma har Maryam da shi kansa gabobinsu sun yi sanyi."
Tana gama isar da saƙon ta fice.
Inna ce ta shigar da kayan hannunta cikin ɗaki sannan ta fito "Mudi tashi mu je ba mu ga ta Zama ba."
"Ke dai ki je in abun ya dame ki, Amma ni kam ina nan ina zaman jiransu, dole sai sun ɗanɗana kuɗarsu 'yan iska kawai, ni za su zubarwa jini a cikin gida, wato su ga sabbin 'yan daba ko?"
Cike da jin takaicin kalamansa ta shura takalminta ta bar gidan bako sallama, a ranta tana faɗar "Bansan sai yaushe ne Mudi zai gyara halayyarsa ba, shi kullum ba ya furta kalmar alkhairi ga ƴaƴansa sai ta lalaci, bai san hakan ke ƙara lalata su ba."
A taƙaice dai kwanansu uku a Asibiti ba tare da Mudi ya leƙa su ba, a wuni na huɗun ne da yamma Lis Inna ta tattaro ƴaƴanta suka gudo daga Asibitin sakamakon ba su da kuɗin da za su siye magani, shi ne likitoci suka bar su nan a yashe, gashi har lokacin Mudi bai leƙa su ba acewarsa "Duk tsuntsun da ya ja ruwa ai shi ruwa kan doka."
Cike da jin haushin wulaƙancin da aka masu ta yo gida da su.
Alhamdulillah! Jikin Sofi ya yi kyau, kasancewar ita ɗinki ne aka mata a gaban Goshi, an bar ta ne ta huta dama.
Hanifa ce bata da ƙarfi kwata-kwata, ɗinki aka mata a gefen cikin ga shi sai da aka mata ƙarin jini, saboda ta zubar da shi da yawa.
Ko a Napep hanyarsu ta dawowa ma sai hararen juna suke daga nesa-nesa, Inna bata kula ba,Maryam ce kaɗai ta ankara da hakan.
Lokacin da suka ƙaraso gidan Baba ba ya nan don haka hankali a kwance Inna da Maryam suka shigar da su ɗakinsu tare da kwantar da su.
Hanifa ko dogon motsi ba ta yi saboda barazanar fitowa waje da kayan cikinta ke yi. Ji take kamar ɗinkin zai farke...
Tana nan kwance ta ji ringin ɗin wayarta da tuni ta manta a wace duniyar ta bar ta. Haƙiƙa in lokacin rasa abinka bai zo ba ko a kasuwa ka ajiye ba mai ɗauka, domin da ba don haka ba tana da yaƙinin ba zata riski wayar ba, adai yanda ɓeraye masu ƙafa suke yawo a gidan inda suka ga dama.
"Maryam don Allah miƙo mun wayar can." Ta faɗa.
Maryam da har ta kai ƙofa ta juyo ciki da sauri, takawa ta yi zuwa inda wayar take cikin wata tsohuwar jaka. Ciro ta ta yi ta miƙawa yayar sannan ta fice.
A dai-dai lokacin ne kira ya shigo wayar a karo na biyu "Waye zai takura mun ina fama da kain......"
Sauran maganar ce ta maƙale a can ƙasan maƙoshinta don ganin mai kiran HAJIYATA shi ne sunan dake yawo a saman fuskar wayar, sarai ta gane mai kiran Alhajinta ne wato Alhaji Saminu. Ta na son ɗagawa ko don ta sanar masa da halin da take ciki, sai dai kuma ba hali tunda ga Sofi kwance kusa da ita.
Tana nan tana tunani har wayar ta tsinke, kira ya kuma shigowa a karo na uku.
Sai da ta aikawa Sofi saƙon harara kafin ta daga wayar cikin Sarrafa harshe "Assalamu alaikum Hajiyata."
Daga jin haka Alhaji Saminu ya ƙyalƙyale da dariya domin ya tabbatar tana ɓoyon kurwa ne don kar wani ya gano halin da take ciki.
Hakan tasa ya ce "A'ah! Yau Babyn tsolaya ake ji? Ba wannan ba ina kika shiga ne na yi ta kiran ki kusan kwana huɗu kenan ina kiran ki bakya amsawa?"
"Uhmm! Ki bari Hajiyata na shiga dawa ne yin wata farauta, sai dai tafiyar bata yi kyau ba domin saura kaɗan Kurar ta kai ni ƙasa, amma dai yanzu haka ina kwance a gida ina jinyar raunukan jikina."
Da yake shi ma Alhajin ɗan bariki ne kai tsaye ya gano manufarta ya ce "Assha! Dawa bata yi nama ba kenan, to Allah ya kyauta yanzu yaushe za mu haɗu?"
Murmushin takaici ta yi ta ce "Hajiyata ki manta da wannan maganar yanzu ko zama bana son yi saboda barazanar farkewa da cikina ke yi, amma idan na ji sauƙi zan karɓa gayyata." Cikin raunanniyar murya take zancen.
Gano cewa tana cikin raɗaɗi da zogin ciwo ya sanya shi yi mata sallama tare da alƙawarin aiko mata da kuɗin jinya.
Da Hanee tasan halin da ƙwaƙwalwar Sofi ke ciki tabbas da bata wahalar da kanta gurin canza salon magana ba. Domin kuwa tuni Sofi ta faɗa duniyar tunanin kyakkyawan saurayin da ta ci karo da shi kwana biyar da suka wuce. Idanunta sun kasa mantawa da kyakkyawar surarsa mai kayan kallo kunnuwanta sun kasa mantawa da zazzaƙar muryarsa mai daɗin sauraro, muryarsa ta ci gaba da yi mata amsa amo a kunne "Ka da ki sake haɗuwarmu ta gaba ta kasance haka domin komai zai iya faruwa."
Kyayataccen murmushi ta saki a fili ta ce "Koma me zai faru a yayin haɗuwa ta gaba, zan so zuwan wannan ranar."
Daidai lokacin da Hanee ta kashe wayar ta ɗago tana kallonta sake da baki. Ita dai tasan a zahiri su biyu ne a ɗakin, to da wa Sofi ke magana? Ta kasa fuskantar inda kalamanta suka dosa.
A tsakar gidan kuwa Inna ce kwance saman wata tsararriyar tabarma yara sun kewaye ta sai kukan yunwa suke mata, anan Sadik ya ce "Inna da kuna asibiti mun sha wuya sosai, Baba baya ba mu komai sai zaginmu da yake, Gidan Baba ƙarami Kawai muke zuwa a samana abinci da dare kuma mu kwana nan tare da Baba. Ai dai ba za ku koma ba ko?"
"Me zai maida mu inda ba a san darajar ɗan adam ba? Yanzu zamanin nan in baka da kuɗi mahaukacin kare sai ya fika ƙima a idon duniya." Ta furta da ɗan yanayin damuwa.
Basma ta ce "Inna gaskiya mu yunwa muke ji a ba mu abinci."
Murmushin yaƙe ta yi ta ce "Sai ku jira zuwan Baban naku tunda kun ga mai bayarwar ciwo ya kwantar da ita bare ta yi kitso ko lalle mu samu na abinci."
Kuka suka saka mata ta masu banza sai ma gyara kwanciyarta da ta yi.
Ana tsaka da haka ne Baba ya shigo gidan. Ko da ya samu labarin dawowarsu ya hankaɗa tsumman labulen cikin fushi ya tsaya ƙerere akansu.
"Ku 'yan iska tijararru! Wato ni kuke ƙoƙarin yiwa kisan kai a gidana ko? To yau zaku ga abinda zan muku a cikin gidan nan."
Jin sautin Muryarsa ya razanar da su duka har ba su san lokacin da suka haɗe da juna ba, kowaccensu ta yi wiƙi-wiƙi da ido.
Sun sani sarai kaɗan daga cikin aikin Baba ne ya kirawo Baba dan lami(ƙaninsa) ya jibgesu a banza.
"Yau ni da kaina zan gwada sauran jarumtata akanku in har baku gaya mun wanda ya baku izinin yin dambe a cikin gidan nan ba."
Fita waje ya yi ya rarumo wata sharɓeɓiyar bulalar ice ɗanya, ya yi kansu gadan-gadan yayin da Inna ta biyo bayansa tana ƙoƙarin dakatar da aika-aikar da yake son yi...
managarciya