WATA UNGUWA: Labarin Haɗarin Rayuwar Bariki da Masha'a, Fita Ta Farko
*WATA UNGUWA*
*(Labari game da wata hargitsattsiyar unguwa mai cike da abubuwan mamaki da al'ajabi)*
Alƙalamin: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)
Marubuciyar: SOYAYYAR MEERAH.
*YAR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA(GAJEREN LABARI)*
*HALITTAR ALLAH CE*
AND NOW
*WATA UNGUWA*
GODIYA: Dukkan godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki buwayi gagara misali Sarkin da ya aramun rayuwa da lafiya ya kuma bani basira da damar rubuta wannan littafi domin ya zama faɗakarwa da jan hankali a rayuwa al'umma baki ɗaya.
Tsira da aminci su ƙara tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam
Tare da iyalan gidansa da sahabbansa baki ɗaya.
*Gargadi:* Ban yarda wata ko wani ya canza mun labari ta kowacce siga ba ba tare da izinina ba.
*AREWA WRITERS ASSOCIATION*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Free page
P 1
BABI NA ƊAYA
GARIN MAMBIYA
UNGUWAR GARWA
Da misalin ƙarfe 6 na safiyar ranar Lahadi unguwar ta yi tsit baka jin motsin komai sai na iskar dake kaɗawa, titin ya yi tsit kamar ba wani mahaluƙi dake rayuwa kusa da gurin.
Bayan shuɗewar mintuna biyu sai ga wata dalleliyar baƙar mota ta hawo titin da alama matuƘin motar ya na cikin hanzari ne. Can kuma motar ta ci burki dai-dai kan wani ƙaramin layi.
Daga cikin motar wata matashiyar budurwa ce da ba zata haura shekaru 20 ba zaune a mazaunin mai zaman banza, Juyawa ta yi ta kalli wani babban mutum dake zaune a mazaunin Direba ta ce "Ya Alhaj ni zan ƙarasa gida ka san halin mutanen unguwar nan, da na sake wani ya ganni shi ke nan na shiga uku."
Yar dariya ya yi sannan ya kuma dubanta ya ce "Haba Hanee Baby daɗina dake masifar tsoro, don kin sha daɗinki a waje miye?"
Tamke fuska ta yi tare da ɗora hannu kan Mabudin ƙofar motar zata fita. Cikin zafin nama Alhaji Saminu ya riƙo hannunta yana Faɗar "Haba habah! Hanee Baby ki yi haƙuri na daina kawo jakarki na saka miki kuɗin hajarki."
Banza ta masa kamar bata ji ba ya ɗauki jakar dake kan cinyarta yana murmushi irin na yan bariki, ya ciro kuɗi daga gaban motarsa Bandir na yan ɗari biyar-biyar rafa ɗaya ya saka mata a jaka, ya miƙa mata jakar.
Karɓa ta yi ta fita daga motar ba tare da ta ce komai ba.
A zahirin gaskiya gangar jikinta ce kawai take a gurin amma ruhinta yana gun tunanin me zai je ya dawo idan wani ya gan ta.
Sanye take da baƙar abaya amma a cikin jikinta riga da wando ne ɗamammu wanda sai ka aje hankalinka sosai zaka lura da hakan.
Tana fitowa ta ji wani irin sanyi na ratsa gaɓoɓin jikinta ta yanda har yake shiga ƙasusuwan jikinta.
Waige-waige ta hau yi ganin ba kowa ya saka cikin hanzari ta shige layinsu tana tafiya gudu-gudu sauri-sauri.
Abunda bata sani ba shi ne ashe tun lokacin da Alhajin ya faka mota Mamuda s/m yana zaune ketaren titin ya na kallonsu.
Tun lokacin da aka fito daga sallar asuba kowa ya koma gidansa ya rufe saboda tsananin sanyin da aka tashi da shi amma ban da Mamuda wanda ya Shimfiɗa ƙyalle ya zauna duk ya takure jikinsa saboda sanyi, amma baya son ya shiga gida don kada wani ya zo ya wuce ko ya yi wani abun bai gani ba tsabar munafunci.
Ya na ganin shigewar Hanifa layin ya miƙe tsaye ya na Faɗar "Kai! Ashe kura ce muke gani da fatar Akuya dama wannan yarinyar 'yar bariki ce? Ba mamaki...
Dariyar jin daɗi ya yi sannan ya koma ya zauna yana Faɗar "na samu rahoto na ɗaya bari na zauna ko a samu na tarawa."
Lokacin da Hanifa ta isa gida ta tarar da ƙofar gidansu a rufe kamar dai yanda ta yi tsammani hakan ya saka ta yi sauri ta kewaya ta hanyar da ta tanadarwa kanta saboda hakan, ranta fal tsoro ta taka dutsen ta haura kan katanga sai gata cikin gidan tsulum.
Ajiyar zuciya ta sauke da ƙarfi "Hmmm!" sannan ta wuce saɗaf-saɗaf ta nufi hanyar ɗakinsu.
Har ta wuce ɗakin Inna kamar yanda ta yi tsammani suna nan suna barcin asarar da su ka saba, dama Baba sallar Asuba bata dame shi ba sai ƙarfe takwas na safe ma watarana yake yi bare kuma ya tsawatar masu.
Bai fi saura taku biyar ba ta shiga ɗakinsu kamar daga sama ta jiyo a bayanta "Kambu.... Ashe ba a gida kika kwana ba?" Ta jiyo Muryar yayanta Mankas yana faɗa cikin muryar 'yan daba.
Tsuru-tsuru ta yi tana kallonsa shi kuma ya matso kusa da ita ya ce "Daga ina ki ke? Bari Baba ya tashi yau akwai kallo a gidan nan kenan."
Sanin halin yayan nata ya saka ta ɗan haɗe fuska ta ce "Matsalata da kai kenan baka da sirri, yanzu dai zan baka cin hanci sai ka rufa min asiri."
"Yawwa yarinya da kinwa kanki adalci." Ya faɗa.
Jakar hannunta ta buɗe tana ƙoƙarin lalibo masa kuɗi shi kuwa ya zuro kai yana leƙen kuɗin. Ko da y kyalla ido ya ga kuɗi da yawa sai ya sake baki kamar wani gaula, har ya buɗi baki zai yi magana kenan ta ɗunguna masa dubu ɗaya a hannu ta ce "ga shi sai ka sake mun kurwa ko?."
"In kin isa Allah ya tsinen, in ga kuɗi da yawa ki bani dubu ɗaya rak, ko an gaya maki wannan kuɗin ne zai ishe ni yin chaji? Gama yau muna da wani ofireshin da zamu fita tun safe."
Cuno katon bakinta ta yi tana faɗar "Haba Mankas, Ni ka san wahalar da na sha kafin na samu kuɗin?."
"Ok ajiye kayanki a jaka bari in ta so Baba."
Daga murya ya yi yana Faɗar "Baba!, Baba!!."
Cikin hanzari da rawar baki Hanifa ta ce "Don Allah Mankas yi shiru zan ƙara ma."
"Kin kyautawa kanki."
Cikin ƙunƙuni ta dauko dubu biyu ta ƙara masa, tana 'yan maganganu can ƙasa-kasa yanda ba zai ji ba.
Da bata da niyyar ƙarasa masa amma sanin jaraba irin ta Mankas ya saka ta bashi, ta yi sauri ta ƙarasa ɗaki tana faɗar "Jarababbe kawai, ni Ya Abba yafi mun kai don baya yunƙurin tona ni, mu kashe mu binne ba wanda ya sani. Amma kai a karon banza kana son janyo mun tsinannen duka."
Daga haka ta ƙarasa ɗakin nasu da kallo ɗaya zaka masa kasan yana cikin gidan talakawa ne, domin kuwa ginin bulo ne kawai ko filasta babu har wani bangare na ginin ya fara kwakwarewa.
Abayar ta cire tare da riga da wandon ta naɗe ta tura su can ƙasan bakkon kayanta, sannan ta janyo wani tsumman zanin atamfa da kallo ɗaya zaka masa kasan ya yi kewar ruwa da sabulu, ta yi ɗaurin ƙirji sannan ta haye yagalgalallar katifarsu da ko Shimfiɗa babu ta takure daga can gefe gudun kada ta tashi ƙannenta 'yan mata biyu da suke kwance kan katifar. zama ta yi tana kirga kuɗin da ta karɓo gun farkanta, kawai sai ta ji motsin ɗaya daga cikin ƙananun yaran dake kwance a ƙasa kan tabarma.
Da sauri ta mayar da kuɗin jaka ta
Kwanta kamar mai barci tana ta faman ƙissima abubuwan da zata yi da kuɗin.
Bayan gari ya yi haske Inna ce ta fito daga ɗaki tana ƙoƙarin gyara ɗaurin ƙirjinta, buta ta ɗauka ta nufi bayi bayan ta fito ta zauna a tsakar gidan ta yi arwala sannan ta shiga ciki, a lokacin ta yi sallar Asuba. Har zuwa Lokacin Mudi(Baba) bai tashi daga barci ba bare ayi zancen Sallah ko fita nema, sai kusan ƙarfe goma na safe ya fito ya yi Sallah. Koda Inna ta tambaye shi kuɗin karin kummalo sai ce mata ya yi "Ni yau ko asi bani da, je gun wacce kika saba karɓa gunta."
Bata bi ta kansa ba ta fice sai ɗakinsu Hanifa lokacin duka yaran sun tashi daga barci, sai Hanifa dake ramakon barcin da bai isheta ba daren yau.
Hannu ta saka tana bubbuga kafaɗarta "Hanifa! Hanifa!! tashi ki bamu wani abu mu karya."
Cikin barci da jiyo dukan ta farka tana turo leɓe "oh shit! Habah Inna! Wai miye haka bakya ganin barci na ke?" Ta faɗa tana tashi zaune.
"Kuɗin kari zaki bamu tunda kinsan Uban naki ba bayarwa yake ba sai ya ga dama." Innar ta mayar mata.
Jakarta ta janyo tare da ciro dari biyar guda biyu ta miƙawa innar "Ga shi a siyo abinda za'a siya a kawo mun canji su kaɗai nake da su ma kuɗin da na yiwa wasu mata kitso ne jiya suka biya ni."
"To an gode." Innar ta faɗa har ta juya ta fita ta hankaɗo yagalgallen labulen ɗakin ta ce "Ɗazu Faridar gidan Bargaja ta zo nemanki zancen kitson da kuka yi alƙawarin zaki mata yau da safe, na ce kina barci. Yanzu sai ki aika yaro ya kira miki ita." Daga haka ta juya ta tafi abinta don neman abinda za'a sarrafa.
Ƙanzon shinkafar da suka ci jiya ta gyara aka siyo kayan haɗi innan ta kwaɗanta musu. Shi aka kakkasawa yaran gidan kowa ya ɗauki na shi cikin halamniya suka cinye ba don sun ƙoshi ba.
Ba abunda yafi ɓatawa Hanifa rai irin yanda Baba ya matso kusa yayin da ake rabon kwaɗon ba ko kunya wai a saka mi shi na shi.
Da yamma bayan Hanifa ta sallami yan kitsonta ta je maƙwafta neman ruwan da zata yi wanka. Daƙyar Ladidi ta sammata ɗai da karamin bokitin ƙarfe.
Ta na shigowa gidan bata nufi ko'ina ba sai ƙofar ban ɗakin dake tsakar gidan, har zata shiga ta tuna da sabulu da sosonta, ajiye bokitin ruwan ta yi ta nufi ɗakinsu.
Can bayan minti biyu sai gata ta dawo hannunta riƙe da kwandon soso, sai dai me? Ko da ta ƙaraso ta duba sama da ƙasa bata ga bokitin ruwanta ba, haka kofar ƙazamin banɗakin nasu a rufe take ruf, saɓanin mintuna biyu baya.
"Waye ne a ciki?" Ta faɗa cikin ɗaga murya, sai dai ba alamar wanda ke cikin zai bata amsa.
Tana nan tsaye a gun tana jijjiga ƙafa tare da mamakin waye wannan a gidan nan da ya rainata haka?
Maryam ce ta zo wucewa zata fita, ta ga yayar tasu tsaye.
"Yaya Hanee me ya faru ne?" Ta tambaya.
"Ke wai Ruwan wanka na samo maƙota shi ne daga na shiga ɗaukar sabulu wani wanda ya fi ni jikin wankewa ya ɗauke." Ta faɗa tana kada kai cikin alamun jin masifa.
"Tab ni dai ba ruwana yaya Sofi ce , na ga lokacin da ta shige."
Maryam na gama faɗa ta kaɗa kanta ta fice daga gidan, yayin da zuciyarta ke azalzala mata ta yi azama ta je ta dawo don ganin bidirin da za a sha a gidan yau, ba don ma tana shakkar Mankas ya zo ya tarar bata je aiken shi ba masifa ta faɗa mata da ba abunda zai hana mata kallon wannan series da za'a fara kafcensa a yau.
Bayan kamar mintuna biyar sai ga Sofi ta fito daga bandakin tana yarfe ruwan jikinta.
Cikin azama Hanifa ta yi kanta tana huci tamkar zakanya. Ƙwace Bokitin ƙarfen dake hannun Sofi ta yi cikin shammata ta kwaɗa mata shi a gaban Goshi, sai da jini ya yi feshi.
Wani Uban ihu Sofi ta kwarara tare da dafe gaban goshin nata da tafin hannunta ɗaya cikin Muryar kuka ta ce "Ni zaki fasawa goshi?"
"An fasa miki ɗin, uban wa ya ce ki ɗauke mun ruwa? Kin san wahalar da na sha kafin na same su, ko kin san inda nake shiri za ni?" Ta faɗa tana huci, da ganin yanayin ta ka san ranta ya mugun ɓaci.
"Tab! Ai ko yau zaki ga haukar da yafi naki don sai dai mu yi kare jini biri jini dake a gidan nan." Tana gama faɗa ta wuce da sauri ta nufi madafa tana waige-waigen neman wuƙa, yayin da Hanifa ta ɗauko wata jibgegiyar ƙotar Gatari ta tsaya cak tana jiran Sofi.
Duk wannan bidirin da ake ba kowa a gidan Inna ta ficewarta zuwa ƙauye kamar yanda ta saba duk ranar Lahadi, sai ƙananun yara kawai suma sun fice gun wasarsu Sadik da Basma kawai suka rage a gidan, sai ihu suke suna faɗar "Faɗa na da daɗin kallo, faɗan da ba naka ba tsura ido, Ku kashe kanku a gidan Ba mai raba ku."
Can Sofi ta rarumo wata sabuwar wuka mai kaifi ta nufo inda Hanifa take tana faɗar "Yau sai na fitar miki da jar kala ajikinki kamar dai yanda kika mun."
Hanifa gyara tsayuwar ta ta yi tare da ɗaga ƙotar gatarin tana faɗar "Allah ya baki Sa'a jiki bai fi jiki ba, haka kuma ba ki fini iya daba ba..."
Kafin ta gama rufe bakinta Sofi ta dako zalle cikin zafin nama da Sa'a ta kaiwa Hanifa suka."
Dai dai lokacin Maryam ta Kunno kai cikin gidan, a tare suka saka ihu da Hanifa. Ita tana ihun firgicin data gani Hanifa kuwa tana ihun azaba da zogin da take ji.
Kafin Maryam ta yi wani yunƙuri jiri ya ɗebe su duka suka zube a gurin sumammu..........
Hmm! Wannan labarin salon shi daban ne kamar yanda yake na dabam....
UMMU INTEESAR CE
managarciya