WATA UNGUWA: Fita Ta Biyu
WATA UNGUWA
P2
BABI NA BIYU
A wannan ranar da misalin ƙarfe sha ɗaya na safe, wata ƙaramar yarinya da ba za ta wuce shekaru biyar ba a duniya ce na hango a cikin wani layi tana tahowa daga nesa.
Ba ta sanye da komai face bante fari wanda tsabar dattin da ya yi idan ka gan shi sai ka ɗauka kalar ruwan zuma ne. Fuskarta ta yi face-face da busasshen kunu hancinta dame-dame da majina, kallo ɗaya za ka yi wa jikinta ka fahimci cewa jikinta ya jima bai ga ruwa ba.
Tafe take tana 'yan wasanninta irin na yara har ta zo ƙofar wani gida, turus ta tsaya tana kallon ƙofar gidan. Turawa ta yi ta ji ƙofar a rufe gam.
Da ganin haka sai ta koma gefen ƙofar ta zauna tana kuka da faɗin "Mama! Mama!! Mama!!!"
Wata sassanyar iska ce ta ratsa ta shiga cikin jiki da ɓargonta, ta ƙara takure jikinta guri ɗaya alamun sanyin ya ratsa ta sosai.
Can bayan wani lokaci da ta ga ba alamar dawowar mahaifiyarta yanzu sai ta miƙe ta fara tafiya tana kuka tana shiga gida-gida tana neman maman nata.
Wani gida ta shiga a layinsu ko sallama ba ta yi ba faɗawa kawai ta yi.
Matar gidan tana duƙe tana wanke-wanke kamar daga sama ta ga yarinya tsaye a kanta, ɗagowa ta yi tana duban yarinyar "A'ah! Salma! Lafiya ki ke kuka?"
"Mamata!" Ta faɗa cikin kuka tana mirza ido
"Me Maman naki ta yi ne?" Ladidi ta tambaya tare da tattare hankalinta gaba-ɗaya a kan yarinyar.
Cikın shessheƙa ta ce "Ita nake nema ba ta shigo ba?"
"Ba ta shigo ba, je ki gidan yaya Hanne ki duba ta." Yarinyar ta fice tana ci gaba da kukanta wiwiwi.
Ita kuwa ta ci gaba da wanke-wankenta tana faɗar "Biba ikon Allah! Yau kuma gantalin ya tashi a unguwa, ko ina ta shiga ta bar wannan kucakar yarinyar tata?"
Ganin ba mai amsa mata ya saka ta ci gaba da aikinta ba tare da samuwar komai ba.
Salma tana fita ta miƙe hanyar da za ta sada ta da layin gidan yaya Hanne (yayar mahaifiyarta) tana shigowa kan layin gidan dai dai nan wani Babur ya danno cikin layin aguje, bai yi aune ba ya kaɗe ta.
Ihu ta ƙwala wanda ya gigita shi, bai tsaya ganin ko 'yar waye ba balle kuma abin da ya same ta, kawai ya ƙarawa babur ɗinsa giya ya fece ya na faɗar "Ku ga yarinya za ta jaza mun bala'i yasin ba zan tsaya ba."
Kawu Sadi da ya shigo layin yanzu ya hango abin da ke faruwa sai dai kafin ya ƙaraso gun tuni mai laifin ya gudu.
Da hanzari ya ƙaraso inda take ya tada ta zaune don duba ko ta ji rauni.
Tabbas ta ji rauni, bakinta ya fashe da jini ɗaya daga cikin ƙananun hakoranta masu kama da haƙoran ɓera ya fita, kanta ya fashe sakamakon ƙumuwa da kan ya yi da dutse yayin da take faɗuwar.
Kan kace me, jama'ar layin sun cika gun an kewaye ta ana ta jimami. Wani ƙaramin yaro ne na ga ya juya da gudu ya shige wa gida a layin yana haki kamar wanda ya shiga gasar tsere, zuwa jimawa kaɗan sai ga shi ya dawo tare da Biba da yaya Hanne yana nuna musu wurin da yatsa.
"Innalillahi wa innailaihir raji'un! Salma me ya zo dake nan?" Ta faɗa kamar za ta fashe da kuka ta rarumi 'yar ta zuwa shagon magani mafi kusa.
Sun mata duk taimakon da ya dace sannan ta saɓa 'yar ta a baya ta nufi gidanta.
A hanya ta haɗu da Abba, yake tambayar Abin da ya faru. Ƙarya ta yi masa da cewa faɗuwa Salmab ta yi. Ya jajanta mata ya wuce abinsa.
Ƙofar gidan ta buɗe da maƙulli sannan ta sa kai a cikin gidan.
Tsakar gidan ya yi kaca-kaca tamkar makwancin Jaka. Kwanuka ne ga su nan birjik wasu har sun bushe, sai ƙuda ke bin su buuu!
Tana giftawa za ta wuce ƙuda suka tashi buuu, sai sautin kukan ƙudaje kake ji.
Wuce wa ta yi zuwa ɗakinta tana faɗar "Don Allah ji yanda ƙudaje suka cika gida kamar inda aka yi kashi, ni waɗannan banzayen ƙudajen da zan samu maganin kisan su da tuni na ƙarar da su mtsw! Ta faɗa tana jan wani uban tsaki.
Shi ma ɗakin ba ya shaƙuwa ban da zarnin fitsarin yara ba abin da ke tashi a ɗakin.
Wani tsumma ta shimfiɗa ta ajiye yarinyar sannan ta fita waje tana faɗar "A'ah! Yau dai har yanzu ba wacce ta shigo gidan nan, ga lokaci yana tafiya ban ɗora komai ba har cikina ya fara kiran ciroma."
Can kuma ta miƙe ta nufi waje tana leƙen ƙofar gida, ɗaurin kirji ne a jikinta kanta ba ko ɗankwali. Sadik ta hango zai wuce nan ta sa baki ta kira shi. "Kai Sadik zo nan."
Ƙarasowa ya yi bai yi magana ba sai ita ce ta dube shi ta ce "Idan ka je gida don Allah ka ce ina kiran Hanee da Sofi, ina nan ina jiransu yanzu."
"Gaskiya ba gida zani ba, bari dai zan biya na kira sun."
Murmushi ta yi har ƙazaman hakoranta suka bayyana tana faɗar "Yawwa ƙaninmu yi sauri ɗan albarka."
Bai bi ta kanta ba ya wuce ya nufi hanyar gidan.
Da har za ta juya ciki ta hango ɓullowar Nazee, ƙara maƙewa ta yi yanda ba zai hango ta ba gudun kar ya gudu.
Sai da ya zo daf da ƙofar gidanta sannan ta dawo dai dai inda take a ɗazu ta ce "Nazee namu don Allah zo ka ji."
"Me zan ji ne? Yau dai haka za ki ganni ki bar ni Biba..." Ya faɗa mata a gadarance yana mata kallon uku saura kwata.
"Habah! Nazee Biba ce fa, kai kasan wannan harƙallar yanda take duk cuɗe ni in cuɗe ka ne, zo ka ji don Allah." Ta faɗa tana yashe ƙara haƙora.
Ganin ba shi da mafita ya taka zuwa soron gidanta ita kuwa ta koma daga ciki "Ga ni miye?" Ya faɗa yana haɗe fuska wai don kar ta ga damarsa.
Ba ta damu da hakan ba ta ce "Nazee don Allah ɗari uku za ka ba ni in yi cefane, yau haka Habibu ya fice bai ban komai ba, ban da shinkafar dake ajiye."
"Mijin naki ma ya kasa baki ni me zan iya miki to?" Ya faɗa fuskarsa ba yabo ba fallasa.
"Taimako dai za ka yi irin wanda ka saba, in na dafa ma zan ajiye maka yasin."
Ganin dai Biba ba za ta taɓa sake masa kurwa ba in dai ba bata ya yi ba, hakan ya saka ya ciro wata cukurkuɗaɗɗiyar ɗari biyu daga aljihunsa ya miƙa mata yana faɗar "Iya wannan za ki samu a wajena, kuma Allah ya tsare ni da cin ƙazamin abincinki." Ya juya ransa a ɓace, don zuwa lokacin Biba ta gama zuwa masa wuya dama kawai yake jira don ya yi amfani da ita ya fincike ta cikin rayuwarsa, ya gaji da halin banzan ta na roƙo.
Yana jinsa sanda ta ke cewa "Shege na ji dai je ka ba dai ka bada ba."
Komawa ciki ta yi tana faɗar "Aha! Ka ga yanzu na samu ƙari sai na yi cefane da wannan, ɗari biyar ɗin da Habibu ya bada ta cefane kuma in sa a bankina, gwanda na tara kuɗin ankon nan da wuri, shi mai zurfin ido daga nesa yake fara kuka. Allah ya kawo mun Hanee na san zan samu ƙari a wajenta." Murmushi kawai a tunaninta ta ci banza.
Bayan mintuna talatin sai ga Sofi ta shigo gidan.
"Yawwa Sofinmu zo ki ji."
Me zan miki kuma?" Ta tambaya a gadarance.
Don Allah kwanukan nan za ki wanke mini, girki zan ɗora yanzu ga shi ba kwano ko ɗaya a gidannan nan duk sun yi datti." Ta furta tana nufar madafar don ta ɗauko sauran tukwane masu dattin da ke ciki.
"Tab ai ni ba jakar gidanku ba ce da zan ci wannan uban wanke-wanken ni kaɗai." Ta mayar wa Biban tana ƙoƙarin zama kan tsumman tabarmar dake shimfiɗe a tsakar gidan tana taɓe baki da bin kwanukan da kallo a ƙyamace.
"Habah Sofi ki yi haƙuri, yasin zan saka abincin da ke, ki ci sai kin ƙoshi don na san ko kin je gida ma ba samu za ki yi ba." A haka ta ci gaba da lallaɓa Sofi har ta shawo kanta ta amince za ta mata.
Nan Sofi ta shiga haɗa kwanukan yayin da ita kuma ta fice zuwa cefane. Bayan wani lokaci sai ga ta ta shigo gidan tana faɗar "A'ah! Wai ni kam har yanzu Hanifa ba ta shigo ba? Wai me take yi ne haka?"
Taɓe baki Sofi ta sake yi tana faɗar "Tana can tana kitson kan wata mata, baki ga kan ba kamar an ci goriba da wuƙa, shi yasa ni ba ko wanne kai nake kitsawa ba."
Dariya sosai Biba ta yi yayin da take ƙoƙarin haɗa wuta "Gaskiya Sofi ba ki da kirki."
Kusan awa huɗu Sofi ta kwashe gidan kafin ta tafi gida bayan ta cika cikinta dam.
Lokacin ne tana shiga gida ta tarar da ruwa a ƙofar banɗaki ba tare da sanin ko na waye ba ta sunkuci bokitin ta yi ciki a ranta tana faɗar 'Rikici ba gado ba kowa ya kwana lafiya shi ya so, in na fito koma ruwan waye sai a yi wacce za a yi. Mai rabon ganin baɗi dai sai ya gani.'
Shi ne fa wannan rikicin ya ɓarke da ma ita fitina bacci take yi kuma Allah ya la'anci mai tashin ta.
Da misalin ƙarfe tara na dare Habibu ya nufo gida tun daga bakin titin unguwar wani ya tare shi ya ba shi labarin abin da ya faru da 'yarsa.
Hankali a tashe ya nufo gida, kafin ya ƙaraso gida ya ci karo da wasu mutum uku waɗanda suka tarbe shi da labarin sai dai kowa yanda ya wassafa masa aukuwar lamarin dabam. Don kuwa a cikin mutanen har da irin wadannan yan ƙarawa miya gishiri.
"Assalamu alaikum." Ya shiga gidan da sallamarsa, sai da ya yi sallama sau uku ba a karɓa masa ba amma yana jiyo sautin dariyar su sai ƙyaƙyatawa suke, dariyar matarsa ta fi ta kowa tashi.
Hakan ya sosa masa rai don haka ba tare da tunanin komai ba ya faɗa ɗakin ba sallama. Tsawa ya yi cak kamar an dasashi a wurin, ya sake baki yana bin falon da kallo kai da ganin yanda ya yi kasan ya ga wani abun da ya matuƙar ba shi mamaki ne.
Ba komai ya gani ba face Nura (yaron maƙotansu kuma ɗan uwansa) zabgegen saurayi ne don zai kai shekaru ashirin da uku a duniya kwance yake kan kujera mai cin mutun uku shi da Sagira (yarinyar layin) sun yi kai da ƙafafu ma'ana dai kansa na wajen ƙafafunta ita ma kanta na gun ƙafafunsa suna fuskantar juna , kanta ba ko ɗankwali suna daman ƙyaƙyata dariya.
Sauran 'yan mata biyu suna kwance a ƙasa yayin da Biba ke zaune a tsakiyarsu da ɗaurin ƙirji, sai suɓalewa zanin yake tana kamawa.
Daga can gefe kuwa 'yarsa Salma ce a yashe kan ledar ɗakin ba ko shimfiɗa ga filasta a goshinta sai bacci take shaka abn ta, ba ta ko san wainar da ake toyawa a ɗakin ba. Sai dai kallo ɗaya za ka yi mata ka fuskanci ba ta jin daɗin baccin domin sai mutsu-mutsu take ta yi zufa sharkaf, duk da cewa akwai fankar chaji a ɗakin kuma aiki take, sai dai iskanta ba ya isa gunta saboda fankar tana fuskantar su Sagira ne, alamar don su aka kunnata.
Ko da suka lura da wanzuwarsa a ɗakin sai suka miƙe kowa ta ja hijabinta sumi-sumi suka bar ɗakin.
Nura ne ya zo ficewa sadda kai ƙasa ya yi yana faɗar "Sannu da zuwa yaya."
Har ya sa kai zai fice daga ɗakin Habibu ya damƙo hannunsa sosai kamar zai tsinka masa jijiyoyin hannu ya na Faɗar "Dakata!"
Kallo ɗaya za ka yi wa fuskar Habibun ka tabbatar cewa ransa ya kai ƙololuwa gun ɓaci, zai iya aikata komai a wannan lokacin.
Ku biya biya kuɗinku ta wannan account ɗin
Account name: Ruƙayya Ibrahim lawal
Account number: 0431343346
Gt bank
Ko kuma ku turo katin waya (Mtn) wannan number:08109634202
Sai kuma ka yi screenshot ka tura shaidar biya ta wannan number: 08109634202.
managarciya