WATA UNGUWA: Fita Ta 25

WATA UNGUWA: Fita Ta 25

BABI NA ASHIRIN DA BIYAR

 

A kiɗime Habibu ya cicciɓi 'yarsa ya fice daga gidan ba tare da ya kalli inda mahaifiyarta take ba.

Su na isa asibitin aka karɓe ta da gaggawa aka shigar da ita ciki tare da yin gwaje-gwaje a kan cutar da ke addabarta.

Bayan wani ɗan lokaci likitan ya fito, sannan ya dubi Habibu "Biyo ni mu je office."

Fuskarsa na bayyanar da matsananciyar damuwa ya bi bayansa.

Bayan sun zauna likita ya kalle shi cikin fusata "Wannan yar kuwa kai ne mahaifinta?"

 

Da mamaki Habibu ya gyaɗa masa kai alamun tabbatarwa.

"Amma dai matar uba ke rainonta ko kuma a hannun dangi take?"

 

"A'a likita, tana ƙarƙashin kulawar mahaifiyarta ne, kuma a gidana." Ya amsa cike da ƙosawa da tambayoyin rainin hankali da likitan ke yi masa.

 

"Da mamaki kam, wace sakaryar uwa ce wannan?" Likitan ya furta da mamaki.

 

"Haba likita! Na biyo ka nan ne don na ji bayanin halin da yata take ciki ba don ka ci mini fuska ba." Ya faɗa a ɗan fusace.

 

Likitan ya saki fuskarsa kaɗan ya ce "Ka yi haƙuri bawan Allah, abin ne ya matuƙar fusata ni ta yadda har mahaifiyar yarinyar ta yi sake haka, har aka lalata mata rayuwar ya da ƙarancin shekarunta."

 

Ya numfasa sannan ya ci gaba, "Bincike ya nuna akwai mai aikata aika-aika akan yarka, hakan kuma ya yi sanadiyar lalacewar budurcinta tun a wannan stage da take."

Sai ya yi shiru yana nazartar Habibu. Habibu ya zabura da ƙarfi "Kana nufin fyaɗe aka yi wa 'yata Salma?"

 

"A'a, kusan dai haka, an yi amfani ne da hannu wajan lalata." Ya faɗa murya a sanyaye.

 

"Inalillahi wa Inna ilaihir raji'un!" Ita ce kalmar da Habibu ke yawan maimaitawa. Da kyar likitan ya tausashe shi tare da bashi baki har ya nutsu sannan ya shiga yi masa bayanin mafita.

 

"Yanzu zaka barta anan domin ta ci gaba da samun kyakkyawar kulawa daga likitoci, zamu ɗora ta akan magungunan da suka dace, in sha Allah zata warke garas kamar ba abin da ya faru."

 

"Shike nan likita  na gode, amma zan iya ganinta yanzu?"

 

"Eh zaka iya, amma na barta tana bacci."

 

Tun a hanya Habibu ke tafe yana cika da batsewa, kallo ɗaya zaka masa kasan baya cikin hayyacinsa, ikon Allah ne kawai ya kai shi gidansa. A ƙofar gida ya ci birki da Babur ɗinsa, ya sauka tare da shiga gidan a fusace faram-faram.

 

Sautin buga ƙyauren Kofar da ya yi da ƙarfi ne ya tada Biba daga baccin da ya fara samamenta, ta fito a tsorace don ganin meke faruwa.

 

"Sannu mara mutunci, Allah ya waddan halinki Biba, da ranki da lafiyarki kika yi sakaci har wani ya ɓata miki rayuwar yarki, kaicona na yi nadamar auren ballagaza." Ya faɗa cikin ɗaga murya.

 

"Ya isa haka Habibu, don kana aurena ba shi zai baka damar ka zage ni ko ka ci mini fuska ba, ba zan lamunci hakan ba sam. Kuma ni ba ballagaza ba ce kada ka...."

 

"Idan ban kira ki ballagaza ba da limamiya zan kira ki? Ko dabba ma tana kula da ƴaƴanta, saɓanin ke da kika kasance mutum mai halin dabbobi."

 

"Habibu! Wallahi zan aro hali, na kacalcala mutuncinka..."

 

Bata samu damar ƙarasawa ba saboda saukar gigitaccen mari da ta ji a kuncinta."

 

"Ki je gida na sake ki saki ɗaya...." Ya sauke yana huci.

 

Tana dafe da kunci ta dago fuskarta ɗauke da yanayin tashin hankali ta ce  "Ka ƙara sakina Habibu? Bib...biyu fa kenan yanzu?"

 

"Wanne shi ne hukunci mai sauki da zan iya yi maki albarkacin Yayana, ki tattara ki bar mini gidana kafin na ƙarasa tsinka igiyar dayar data rage."

 

Yana gama faɗa ya fice ya barta nan a tsaye cikin jimami da matsananciyar damuwa.

'Yanzu wai gida zan koma? Nasan Abbanmu kashe ni ne kawai ba zai yi ba. Ba ma haka ba wane hali yata take ciki? Me ya same ta?'

 

Haka ta ci gaba da zancen zucinta, da kamar ba zata tafi ba, komai ta tuna Oho, kawai sai ta juya ciki ta shiga haɗa kayanta dana jinjirinta......

 Ummu inteesar ce