WATA UNGUWA: Fita Ta 20

WATA UNGUWA: Fita Ta 20

BABI NA ASHIRIN

_IDAN ANA CIN ƘASA..._

A motarsu da ake yiwa kirari da shiga ba biya fita da Allah Ya isa suka jefa ta sauran 'yan sandan suka ɗare cikin hanzari. Direbansu wanda shi ma yake sanye da kakin yan sanda ya tada motar, Maman Fa'ee sai ihu take tana dakatar da su amma ina ko saurarenta ba su yi ba.

Bayan motar ta wuce sauran mazauna gidan na bargaja suka juya ciki, wasu na dariya wasu kuma suna jajanta mata faruwar lamarin.

A gurin ta ci gaba da tsayuwa cikin tashin hankali a bayyane ta ce "Yanzu ina zan same ta kenan? wace hukumar zasu kai ta?"

Wani matashi na unguwar dake tsaye a bayanta ya girgiza kai, cikin tausaya wa ya tako zuwa gabanta ya ce "Mama ki yi haƙuri da abin da ya faru. Amma ni na san inda zasu tun da ga sunan station ɗinsu a jikin motar."

"Yaro taimaka ka faɗa mini sunan gurin." Ta faɗa tana share hawayenta.

"Guza Station dake unguwar Saminaka a can zaki same su." Cikin tausayawa.

"To yaro na gode, amma ƙarin alfarma ɗaya don Allah ka jira ni na shiga gida na fito sai na tare abin hawa ka kwatanta masa gurin."

Lokacin ana gab da sallar magariba ta juya ciki, bayan 'yan mintoci ta fito ta sami yaron yana jiranta, tana fitowa ya tare masu abin hawa suka shiga. Ba su zame ko'ina ba sai Guza station. Yana nuna mata ƙofar shiga ɗin ta biya mai Napep kuɗin duka ya juya da saurayin cikin gari ita kuwa ta bazama ciki tana rarraba ido.

Tun da take a rayuwa bata taɓa taka sawayenta a cikin station ba sai yau.

'Yan sanda ne ke ta kai-kawo daga haraba zuwa ciki.

A bakin kanta ta tsaya kopur Adamu ya ce "Meke tafe dake?" "Yata kuka kame shi ya sa na biyo sahu.

"Ya sunan 'yar taki, kuma me kike so yanzu?" Ya tambaya a tsattsaye.

"Sunanta Fa'iza kuma na biyo sawu ne don jin abin da ya saka kuka je har gida kuka kama ta " ta amsa cike da tsiwa.

Ɗayan ɗan sandan dake tahowa daga nesa ya ƙaraso yana tambayar Kopur Adamu abin da ke faruwa.

Adamu ya masa bayani.

Ya gyaɗa kai "Ok, Hajiya an kawo mana ƙarar 'yarki ne akan yunƙurin kisan kai da ta yi."

Maman Fa'ee ta zaro ido ta daki ƙirji "Kisa? Na shiga uku ni 'yarsu jikar Mado."

Asp Ashiru ya gyaɗa kai "Ƙwarai kuwa, wata mata ce 'yar unguwar ku ta shigar da ƙarar cewa 'yarki na yunƙurin kashe 'yarta."

Ta shiga girgiza kai, "Ba gaskiya ba ne yallaɓai, duk zuciya irin ta Fa'ee na san ba zata yi yunƙurin kisa ba. Wace mata ce wannan?" 

"Sunanta Iya Suwaiba, 'yarta kuma Sakina. Zaki iya  zuwa ki ga 'yarki tana Cell." Yana gama faɗa ya juya ya fice daga station ɗin, don yin alwala.

Ta ƙarasa ciki da hanzari lokacin ana ta kiraye-kirayen magariba.

Fa'ee na ganinta ta rusa kuka tana faɗar "Kin ji ko Mama za'a dabaibaye ni da igiyar sharri, daga ɗan faɗan nan na ɗazu da muka yi." Hawaye ya fara sauka kan kumatunta, bata taɓa rayuwa ko da ta minti biyar ba ce a tsare kafin yanzu.

 

"Shi ya sa na ce miki ka da ki kula su, kinsan Iya mai bakin aku ta fi kowa iya Gulma da kutunguila a unguwar, _Fitilar sharri kenan_." Maman ta faɗa tana kallonta cikin tausayawa.

Fa'ee ta share hawayenta "Mama ai na tauna tsakuwa ne don aya ta ji tsoro."

"Ga shi garin saka aya a fargaba kin rasa haƙoran tauna wata tsakuwar ba." ta faɗa tana share hawaye sannan ta ce "karki damu zan je in samu iya in ji dalilinta na kulla miki sharri."

Ta juya ta bar Fa'ee tsaye a Cell ɗin, lokacin da ta dawo gurin kanta an riga an sallame Sallar magariba, a nan ta tarar da Iya mai bakin aku.

 Ta harare ta sannan ta matso, ta ce "Iya me 'yata ta miki kika sa aka kamata?" Iya ta yi 'yar dariya daga inda take zaune shirim kamar rumfa, ta ce "ki tambaye ta ki ji, ko da yake ba buƙata tun da a gabanki ta shaƙe min Ya tana yunƙurin kashe ta baki yi magana ba, sai yanzu."

 Sakina ta birtsono baki, "Wallahi iya tana ɗaki lokacin, kuma ina da yaƙinin ta ji komai amma bata yi yunƙurin raba mu ba, Shamsiyya ma shaida ce."

 "To ta Allah ba taku ba, kuma insha Allah sai Fa'ee ta fita daga wannan tarkon da kuka ɗana mata da izininS...."

 Bata ƙarasa maganar ba saboda shigowar Atika da mijinta gurin Atika ta matsa gaban kantar ta tsaya. Kopur Adamu ya ce "Me ke tafe dake?"

ta  ce "Ni ma na zo shigar da ƙarar Fa'ee ne saboda ta fasa mini kai."

 Ta nuna gurin da aka mata ɗinki akai "Yallaɓai ka ga gurin, wannan yarinyar 'yar ta'adda ce kowa yana da ƙurjinta a gidan."

 "Atika idan kina cin ƙasa ki kiyayi ta shuri kuma ki iya bakinki a nan wajen, ko ki kwashi kashinki a hannu yanzun nan_ don na yi faɗa dake ɗazu ba shi zai baki damar yi wa yata sharri ba, ke ki faɗi abin da kika yi mana manah. Nan fa suka hau cacar baki, kamar zasu buga ganin haka ya saka yan sandan dake wajen suka yi waje dasu tare da masu gargadin cewa "Su kula station ba......

UMMU INTEESAR CE

 

WATA UNGUWA