WATA UNGUWA: Fita Ta 11

Ya fara 'yan ɗauke-ɗauke cikin ruwan sanyi, tun abun bai bayyana ba har ya kai kowa ya shedi wannan halin Ɓeran nasa a unguwar. Suna nan a haka, damuwa ta fara samun matsugunni a zuciyar iyayensa sai kuma suka ji labarin ya fara tsiro da wata sabuwar ɗabi'a ta damfara. Wannan labari Kusan a'iya cewa shi ne mafi munin labari da ya yi silar jijjiga ahalinsu har ma ya yi silar ɗauke musu tsohonsu da ya kasance Babban jigo a rayuwarsu. Domin kuwa Alhaji mijinyawa ya kasa jurar wannan baƙin ciki na yawan ɗebo masu rigima da Mudi ke yi. Ga shi a kwance yana jinya amma a rana sai a masa sallama sau goma duk akan wannan sana'ar banzar da ɗansa ya fara. Wata rana da safe misalin ƙarfe goma Alhaji mijinyawa yace ga garinku bayan ya gama karɓar ƙarar Mudi da aka kawo da mintuna talatin, kuma da wannan tabon ya tafi a ransa.

WATA UNGUWA: Fita Ta 11

BABI NA SHA ƊAYA

 

Kafin Inna ta shigo ɗakin tuni ya fara tsula masu bulalar ba ji ba gani.

 

Nan fa suka gigice suka sake mannewa guri ɗaya tare da ƙanƙame juna ƙam, sai ihu suke don azabar raɗaɗi.

 

Ko da yake abun ne ya masu yawa wai shege da hauka, ga zafin raɗaɗin ciwon jikinsu ga kuma raɗaɗin bulala da yake tsula masu.

 

Shi kuwa ko kaɗan bai damu da duk wannan iface-ifacen da suke ba, Babban burinsa shi ne ya ga ya raunata su, bayan raunin da yake jikinsu. Sai kumfar baki ya ke "Ba ku ga 'yan iska tijararru ba? Yau zaku ga ƙarshen ƙaryar karuwanci da iskanci, wato ku ga 'yan tasha fanɗararru. Waya sani ma ko kun fara yan kurɓe-kurɓen nan na zamani?"

 

Ya daga bulalar zai sake tsula masu kenan, Inna ta shiga tsakaninsu tana ƙoƙarin dakatar da shi, bisa tsautsayi bulalar ta sauka kan gefen fuskarta, wutsiyar  bulalar ta tsokane mata ido. A take ido ya shiga ratatar ruwa.

 

"Waah! Shi ke nan Malam ka kashe ni, dama can idon ya yake bare yanzu?" Inna ta faɗa cikin raɗaɗin ciwo.

 

Ihun da Innar ta saka ne ya dawo masa da hankalinsa a muhallinsa, nan fa ya yada bulalar icen yana faman tambaya "Miye ne haka kuma Luba? Ya kike mana ihu kamar ƙaramar yarinya?"

 

"Malam baka ga yanda ka shauɗa mun bulala a fuska ba? Har fa cikin idona." Ta faɗa da alamun har yanzu tana cikin zafin ciwon.

 

"Ai duk laifinki ne, me ya shigo dake cikin faɗan nan saboda Allah? Ko da yake tun can azal haka kike da shiga sharo ba shanu, dama kuma ke ki ke ɗaure masu ƙugu shi ya sa suka raina ni da yawa, yara duk sun zama fitsararru, da ai ba haka suke ba." Ya faɗa yana huci.

 

A maimakon ya tsaya duba idon nata ko kuma halin da yaran suke ciki kawai sai cewa ya yi "Allah ya sawwaƙa Luba." Daga haka ya kaɗa bujensa ya yi waje yana jin zafin yanda Luba ta shiga tsakaninsa da burinsa na lallasa yaran, ko za su gane cewar shayi ma ruwa ne kala ce ta bambanta su.

 

WAIWAYE

 

ASALINSU.

 

Malam Mudi ɗa ne ga Alhaji Usman mijinyawa wanda ya kasance haifaffen unguwar Garwa ne.

Mahaifinsa ya kasance mai rufin asiri sosai a zamaninsa domin shi bafatake ne, fatauci ne sana'arsa yana yawo gari-gari don kai hajarsa idan ya siyar sai ya siyo ta su ya dawo gida ya siyar.

 

A garin yawon fataucinsa wata rana ya isa wani ƙauye mai nisa a cikin wata jiha mai suna Sambusa, a can ya auro wata budurwa mai suna Mari, bayan lokacin tashinsa daga garin ya zo ya je ya shaidawa iyayenta akan zai wuce da matarsa can garinsu MAMBIYA.

 

Sai da aka kai ruwa rana kafin iyayenta suka amince ya taho da ita. Ita ce Allah ya azurta da haifar ƴaƴa maza guda Biyar mata uku.

 

Shehu shi ne Babba sai Iliya, Mariya wacce suke kira yaya Kande sai shi Muddasiru da suke kira Mudi, Ali(Baba ƙarami) sai kuma Dije Sannan Ummaru(ɗan lami) sannan Auta A'i.

 

Gidan Alhaji Mijinyawa gida ne na jama'a gida ne da aka inganta gininsa cike da soyayya da ƙaunar juna, yaransa sun taso da haɗin kai fiye da zaton mai zato.

 

Hakan nan da baƙo da na gida kowa nasa ne, ko da yake yawon fataucinsa ba ya bari ya share tsawon lokaci tare da iyalinsa, amma hakan bai saka yaransa sun taso cikin wani mummunan yanayi mai kama da yunwa ko ƙishi ba.

 

Gidansa ƙaton gida ne da yake ɗauke da wani makeken fili bayan bangaren da iyalansa ke zaune. Duk lokacin da ya ta shi aurar da ɗaya daga cikin yaransa sai dai ya yankawa ɗan fili shi kuma ya yi gini iya wanda ya ishe shi.

 

A haka duk ya aurar da ƴaƴansa maza banda Iliya da Ummaru da suka rasu tun kafin su kai munzalin aure, sai kuma Mudi da ya jima bai yi aure ba, domin kuwa har ƙaninsa Baba ƙarami sai da ya yi aure, shi yana zaune shiru.

 

A wancan lokaci bayan wasu yan shekaru gaɓoɓin Alhaji mijinyawa suka sake, ga curuta ga yanayi na tsufa bisa ga tilas ya daina fita fatauci tunda har Allah ya masa gyaɗar dogo ciwon bai kwantar da shi ba sai a gaban iyalansa.

 

Lokacin ne kuma komai ya fara ja baya, yanayin walwala ya fara bankwana da gidan.

 

Abun duniya ya taru ya ishi Inna Mari, ga ciwon tsohon mijinta ga nata yanayin ita ma na mayyanta. A ɓangare ɗaya kuma ga Mudi da lamarinsa ya shige masu duhu.

Wasu irin ɗabi'u da halaye ya aro wanda sam ba su haɗa hanya da ɗabi'un ahalinsu ba.

 

Ya fara 'yan ɗauke-ɗauke cikin ruwan sanyi, tun abun bai bayyana ba har ya kai kowa ya shedi wannan halin Ɓeran nasa a unguwar. Suna nan a haka, damuwa ta fara samun matsugunni a zuciyar iyayensa sai kuma suka ji labarin ya fara tsiro da wata sabuwar ɗabi'a ta damfara. Wannan labari Kusan a'iya cewa shi ne mafi munin labari da ya yi silar jijjiga ahalinsu har ma ya yi silar ɗauke musu tsohonsu da ya kasance Babban jigo a rayuwarsu. Domin kuwa Alhaji mijinyawa ya kasa jurar wannan baƙin ciki na yawan ɗebo masu rigima da Mudi ke yi. Ga shi a kwance yana jinya amma a rana sai a masa sallama sau goma duk akan wannan sana'ar banzar da ɗansa ya fara. Wata rana da safe misalin ƙarfe goma Alhaji mijinyawa yace ga garinku bayan ya gama karɓar ƙarar Mudi da aka kawo da mintuna talatin, kuma da wannan tabon ya tafi a ransa.

 

Koda Inna Mari ta ga Mudi na neman ɗauko masu dala ba gammo kawai sai ta yi kurum a ranta ta ce 'yaro inka san wata ai baka san wata ba.'

 

Da yake su mutanen wancan zamani haka suke yi, idan yaro ya ɗauko wata ɗabi'ar lalaci ba barararsa ake ba, cikin ruwan sanyi suke maganin matsalar ta hanyar nemarwa yaronsu taimako gun malamai in kuma sata yake a ɗaure hannunsa ta yanda ko miliyan nawa zaka ajiye su kwana a gabansa ba zai ɗauka ba.

 

Ita ma Inna Mari ta wannan hanyar ta ɓullowa lamarin Mudi, da kanta ta saka ƙawarta Kande ta rakata gidan Malam na gangare suka karɓo masa taimakon.

A cikin abincinsa ta dinga zuba masa yana cinyewa ba tare da ya sani ba.

A hankali maganin ya bi jikinsa kawai watarana sai ya wayi gari ya riski kansa da kasa taɓuka komai a cikin sana'arsa ta damfara, duk wata basirarsa a harkar ya neme ta ya rasa tamkar an zare ruhi daga gangar jiki.

 

Kwatsam watarana sai ga shi ya zowa inna Mari da zancen aure. Zuwa lokacin kuwa ya kai kusan shekaru talatin a rayuwarsa bai taɓa zancen aure ba.

 

Hamdallah Innan ta yi tana ƙara yiwa Allah godiya da ya shiryar mata da shi. A nan ta ba shi dama ya nemo duk yarinyar da ta masa a faɗin garin, ita kuwa insha'allah in abun bai fi ƙarfinta ba zata aurar da shi.

 

ANA WATA GA WATA.....

 

Bayan sati ɗaya sai ga Mudi ya zowa Inna da albishirin cewa ya samu wacce ta masa har ta amince da zancen aurensa.

 

Inna ta yi murna sosai, anan take tambayarsa wace yarinya ce?

Ya ce "sunanta Luba Inna, 'yar kauyen Shabaka ce a nan garin."

 

"Shi ke nan kada ka ji komai zan saka ayo mana bincike akan yarinyar." Inna ta faɗa da fara'arta.

 

Innan da kanta ta je ta samu wasu amintattun mijinta a unguwar suka je har ƙauyen Shabaka don yin bincike.

 

Bayan wani ɗan lokaci suka dawo gare ta bayan kammala binciken.

 

Bayan doguwar gaisuwa da suka yi ta masu sannu da dawowa sannan ta kasa kunne don jin sakamakon bincike.

 

Alhaji Bashiru(aminin Alhaji mijinyawa) shi ne shugaban tawagar 'yan binciken don haka ya gyara zamansa yana ƙara jinjina lamarin da tunanin ta ina zai fara bata wannan labarin.

 

"Kun yi shiru lafiya dai Alhaji?" Innan ta tambaya da 'yar damuwa.

 

Alhaji Bashiru ya yi gyaran murya ya ɗora da cewa "Uhmm! Babu komai hajja Mari, da farko dai abunda nake son na fara cewa shi ne mu yi haƙuri da ƙaddara duk yanda ta zo mana mu saka hannu biyu mu runguma domin fa ba zamu iya canzawa ƙaddararmu muhalli ba, kuma shi lamari na aure dama haka ya gada. Kowaye mutum kuwa in aka ce za'ayi bincike akansa ba a rasa kama shi da kuskure ba ko yaya ne, sai dai in za'a yi ayi kawai."

 

Jin waɗannan kalaman ya sanya jikin Innan ya yi laushi, ta ji a ranta cewa yarinyar bata kirki ba ce sai dai koma miye ya kamata ta ji sakamakon binciken don ta san irin zaman da zata yi da yarinyar in ƙaddarar ta ɗauro da ƙulluwar auren.

 

Don haka ta kalle su "Bincike abu ne mai kyau a yayin aure, kuma ba baƙon abu ba ne, ku taimaka ku gaya mun gaskiya tunda yake har na amince da ku na ɗora muku amanata da ta yarona bai kamata ku mun rufa-rufa ba."

 

Jin wannan zancen nata ya sanya bisa tilas suka feɗe mata biri har wutsiya.

 

A nan suka tabbatar mata da cewa Luba dai ba yarinyar arziƙi ba ce domin kaf garin ba wanda bai shede ta da yawon banza ba, duk wani gida na 'yanbariki dake garin nasu ba wanda Luba bata sheda cikinsa da bansa ba domin nan ne mafakarta. Iyayenta da kansu sun gaji da faɗan sun zurawa sarautar Allah ido.

 

Wannan labari bai yiwa Inna Mari daɗin sauraro ba sam. Don haka bayan tafiyarsu ta kira Mudi ta zaunar da shi akan cewa ya canza mata, ya nemo duk wacce ta masa banda wannan domin bincike ya tabbatar da ba nagartacciya ba ce.

 

Take a gurin Mudi ya ƙeƙashe ido ya daki ƙasa ya kuma baɗawa idonsa toka akan cewa Lallai shi in dai ba Luba ba to ya haƙura da aure a wannan rayuwar ita kaɗai ya ji zai iya aura.

 

Ba yanda Inna bata yi da shi ba akan ya haƙura ya nemawa ƴaƴansa uwa ta gari amma ya saka hannu ya toshe kunnuwansa.

 

A haka ta zura mi shi ido kuma ta amince da auren ba don ta so ba, aka daura auren Mudi da Luba.

 

Sai dai shi ba kamar sauran yaran ba ya ƙi amincewa da zama a gidan mahaifinsa kamar sauran yara bisa ga huɗubar Amaryarsa Luba, ya zo ya tada rigima sai da aka raba gado aka ba shi na shi, sai ya kasance ya gadi ɗaya daga cikin madaidaitan gida ukun da Babbansu ya mallaka bayan wannan.

 

A can Amarya ta tare Inna kuwa tana nan gidan da mijinta ya mutu ya barta a ciki. A lokacin ne kuma Babbar 'yarta mace (Mariya) ta rasu a can garin da take aure.

 

Sai dai me? Amarya bata ganin kan kowa da gashi, haka bata da ragowa ko kaɗan komai tsufan tsoho in ya takata ta iya ramawa bata shayin kowa, Innar ma bata bari ba balle duk wanda ya saura.

 

A haka rayuwa ta ci gaba da gangarawa har zuwa lokacin da Luba ta haifi ɗanta na fari Suleman  (Mankas) bayan shekaru huɗu ta haifi  Usman (Abba) nan ma sai bayan shekaru huɗu ta kuma haihuwa inda ta santalo 'yarta mace baƙa Hanifa bayan shekara biyu ta Haifi Safiya ta yi Maryam sai Hanif sai Hafiz sai Abubakar Sadik da auta Basma.

 

Yaran sun taso ƙarƙashin kulawar mace marar kirki da rashin kula duk wasu ɗabi'u da halayarta ita ce yaran suke koya.

 

Ita bata cika damuwa da sakawa ƴaƴanta ido ta ga abunda suke ba, balle har ta kwaɓe su. Hasalima wani abun ita ke ƙara saka su yin shi. Dalilin kenan da yasa yaran suka taso cikin irin wannan mummunar rayuwa.

 

Ko da tafiya ta fara tafiya Innan ta shiryu ba don Allah ba, sai don ganin an tara zuri'a kuma tana son ganin ƴaƴanta sun zama shiryayyu, amma inah! An bar kyau tun ranar wanka, kuma da yake shi ice tun yana ɗanye ake tanƙwarashi idan ya riga ya bushe to fa sai dai a haƙura kawai, domin kuwa ba zai tanƙwaru ba sai dai a karya shi.

 

Ɓangaren Baba Mudi kuwa baya sakewa yaran fuska ko kaɗan ga duka, abu kaɗan ya ishi ya hau masifa yana jibgar yaro, dukan kuwa bana wasa ba irin wanda zai lahantasu yake masu.

 

 

Daga baya da ƙarfinsa ya fara ƙarewa shi ne yake saka ɗan'uwansa Baba ɗanlami yana jibgarsu da zaran sun yi laifi.

 

Wannan shi ne ya yi silar ƙara fanɗarewar yaran, duk da har yanzu suna tsoronsa......