Wasu Matasa Sun  Kone Gidan Mawaki Rarara a Kano

Wasu Matasa Sun  Kone Gidan Mawaki Rarara a Kano

Rahotanni na nuni da cewa wasu gungun matasa sun ƙone gidan mawaƙi Dauda Kahutu Rarara dake ksn titin giddan Zoo  a Kano.

Wannan ya biyo bayan sanar da sakamakon zaɓen gwamna da aka yi da safiyar yau litinin a birnin Kano, wanda ɗan takara a inuwar jam'iyar NNPP Injiniya Abba Kabir Yusuf ya sami nasara. 
Rarara shahararren mawaƙin siyasa ne  musamman ma a Arewcin Nijeriya.
 
Dauda Rarara ya koma yi wa jam'iyar APC waƙa tun a shekarar 2015 zuwa yanzu , wanda ke yin zamɓo da habaici cikin  waƙoƙinsa.
Wanda hakan ke baƙanta ran magoya bayan waɗanda aka yi wa zambon
Kafin sanar da sakamakon zaben mawakin ya rera wakar zambo ga Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da sabon gwamnan jihar in da yake nuna an kayar da su zabe.