Wasu Matan Sai Sun Bayarda Kansu Kafin A Sanya Su Fim-----Naziru Sarkin Waƙa

Wasu Matan Sai Sun Bayarda Kansu Kafin A Sanya Su Fim-----Naziru Sarkin Waƙa

 Sarkin Waƙa Naziru Ahmad ya bayyana wani hali da harkar wasan Hausa ke ciki wanda shi ne ke sanya lamarin masana'antar Kannywood ke ƙara ja baya don haka ya kamata a gyara.
Sarkin Waƙa a wani bidiyo da ya fitar ya tabbatar da maganar Ladin Cimma gaskiya ne kan ana ba ta 2000 a wasan Hausa in da ya ce wasu ma kansu suke biya aiki madadin a biya su.
"Na rantse da Allah haka ake zaluncin, 2000 ake ba su  wani ma cewa za a yi ya je za a yi masa waya, wasu kuma sai sun biya kuɗi ko wani abu makamancin kuɗi, ko ki ba da kuɗi ko ki ba da kanki.
"A masana'antar wadanda ake baiwa 5000 ko dubu 10 an ba su manya kuɗi, haka wasu ke aikin fa, yakamata a gyara," a cewarsa.
Naziru ya ƙalubalanci wani ya zo ya rantse ba haka ba ne, akwai matsaloli da yawa a harkar saboda son kai ya yi yawa a harkar "Mace a ce sai an yi wani abu da ita sannan za a sanya ta a fim wannan maganar haka take ba ƙarya ba," kalaman Sarkin Waƙa Naziru Ahmad.