Wamakko Ya Roƙi Buhari Ya Kori Gwamnan CBN Emefiele

Wamakko Ya Roƙi Buhari Ya Kori Gwamnan CBN Emefiele

Tsohon gwamnan Sakkwato Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya roƙi shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya kori gwamnan babban bankin ƙasa waton CBN Gwamna Godwin Emefiele saboda kasawarsa a tsarin da ya fitar na ƙayyade cirar kudi a yini da sati.
A hirar da aka yi da shi ya ce tsarin zai haifar da ruɗani a cikin ƙasa.
Ya nuna damuwarsa kan saboda mi Gwamnan ya yi tsaye kai da fata sai ya aiwatar da tsarin ba tare da an wayar da kan mutanen ƙasa a ƙalla shekara ɗaya ba.
Ya ce Gwamnan na tsammanin mutane sakarkaru ne  da za su biyar shi kawai ba tare da fahimta ba.
Sanata Wamakko ya bayyana sake fasalin naira da tsarin fitar da kudi Emefiele bai yi wa gwamnatin tarayya adalci ba.
Ya ce mutanen Nijeriya sun san abin da suke yi kan haka suke damuwa da abin da gwamnan banki ke yi kan tsarin kuɗi kan haka ya zama wajibi a kira shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya saukar da shi kafin ya sanya ƙasar cikin fargaba.