Wamakko Ya Jinjinawa Buhari Kan Zaɓar Abdullahi Adamu

Wamakko Ya Jinjinawa Buhari Kan Zaɓar Abdullahi Adamu
 
Shugaban kwamitin tsaro a majalisar dattijan Nijeriya Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya taya murna ga tsohon gwamnan Nasarawa Sanata Abdullahi Adamu kan nasarar da ya samu ta zamansa shugaban jam'iyar APC na ƙasa a babban taron da aka gudanar Abuja.
Sanata Wamakko wanda yake  waƙiltar Sakkwato ta Arewa haka ma ya taya murna ga sauran shugabannin da aka zaɓa tare da shi da fatar za su taimaki shugaban ga samun nasarar APC a 2023.
Tsohon gwamnan na Sakkwato kuma ɗaya daga cikin jagorori da suka kafa APC a bayanin da maitaimaka masa kan harkokin yaɗa labarai Hassan Sahabi Sanyinnawal ya fitar ga Managarciya ya ce samar da shugabannin da aka yi ta hanyar silhu domin haɗa kan jam'iyya abu ne da ya dace.
Wamakko ya godewa shugaba Buhari kan shugabanci da goyon bayansa ga cigaban jam'iyar APC da ƙasa baki ɗaya.