Wahalar Fetur: Dillalan Mai Sun Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki  

Wahalar Fetur: Dillalan Mai Sun Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki  

 

Kungiyar dillalan mai ta kasa IPMAN ta ce za ta janye ayyukanta ta hanyar rufe gidajen manta wanda hakan zai iya gurgunta harkar man fetur a fadin Najeriya. 

Kungiyar IPMAN, ta ce za ta dauki matakin ne sakamakon rashin biyanta sama da Naira biliyan 200 na 'kudin fiton' man fetur, rahoton Arise News.
Wannan ci gaban dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da karancin man fetur, lamarin da ya janyo hauhawar farashin kayayyaki. 'Kudin fito' kudi ne da ake biya na jigilar fetur daga ma'ajiyar man zuwa yankunan da aka amince a rarraba shi domin tabbatar da daidaiton farashinsa a duk faɗin ƙasar. 
Oliver Okolo, shugaba kuma mai magana da yawun kungiyar reshen Aba ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar bayan wani taron manema labarai a ranar Talata. 
Jaridar The Cable ta ruwaito Okolo ya ce hukumar da ke kula da harkokin man fetur ta Najeriya (NMDRA) ce ta rike kudaden da ake magana akai. 
Okolo ya ce NMDPRA ta gaza biyan bashin Naira biliyan 200, wanda ya taru tun Satumba 2022 duk da umarnin biyan daga Heineken Lokpobiri, ministan albarkatun man fetur. 
Ya ce jinkirin da NMDPRA ta yi na biyan bashin ya haifar da "mutuwar da yawa daga cikin mambobinmu da kuma durkushewar kasuwancinsu". “A matsayinmu na ‘yan kasuwa, mambobinmu sun samu lamuni na banki domin su ci gaba da gudanar da harkokinsu na sayar da mai a cikin lunguna da sako na Najeriya. 
“Sai dai abin takaici ne sanin cewa da yawa daga cikin mambobinmu sun fada fatara, kasuwancinsu ya durkushe sakamakon gazawar NMDPRA na biyansu hakkinsu wanda zai basu damar biyan bankuna bashin da suka karba."