A dokar kasa, zababben shugaban kasa da kuma gwamnonin jihohin suna da kwanaki 60 kacal don nada ministoci da kwamishinoni bayan darewa mulki.
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari shi ya rattaba hannu a wannan doka a watan Maris da ta gabata, Legit.ng ta tattaro.
Kamar yadda kundin tsarin mulki ya tabbatar, nada minista da kwamishinoni tare da tura sunayensu zuwa majalisa don tantancewa dole a aiwatar a cikin kwanaki 60 bayan rantsuwar kama mulki.
Shugaba Bola Tinubu da sauran gwamnoni sun yi rantsuwar kama aiki a ranar 29 ga watan Mayu na wannan shekara, TheCable ta tattaro.
Ya rage saura kwana daya kenan wannan wa’adi ya kare, yayin da rahotanni suka tabbatar cewa jerin sunayen ministocin Tinubu sun isa zuwa majalisar.
Yayin da wasu jihohi suka tura sunayen kwamishinoninsu, akwai wadanda ko alama babu na tabbatar da bin wannan doka, cewar Politics Nigeria.
Daga cikin jihohi 28 da aka fafata da su a zaben da aka gudanar a watan Maris, jihohi 12 ne kadai aka ruwaito cewa sun mika sunayen kwamishinoninsu zuwa majalisar dokokin jihohinsu.
1. Abia
2. Akwa Ibom
3. Bauchi
4. Ebonyi
5. Delta
6. Jigawa
7. Katsina
8. Kaduna
9. Kano
10. Rivers
11. Oyo
12. Taraba
Jihohin da suka gagara tura sunayen akwai:
1. Gombe
2. Enugu
3. Cross River
4. Plateau
5. Niger
6. Lagos
7. Ogun
8. Kwara
9. Borno
10. Adamawa
11. Nasarawa
12. Kebbi
13. Benue
14. Zamfara
15. Yobe





