Umahi ya caccaki dalaget ɗin inyamirai bisa ƙin zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa daga yankin

Umahi ya caccaki dalaget ɗin inyamirai bisa ƙin zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa daga yankin
Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya caccaki dalaget ɗin Kudu-maso-Gabas bisa ƙin zabar ƴan takarar shugabancin ƙasa daga ya kin a zaɓen fidda-gwani na APC da s ka kammala, inda ya ce "kun sayar da ƙuri'un ku".
Umahi ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a mahaifarsa, Uburu, yayin bikin yaye daliban jami’ar King David ta kimiyyar lafiya karo na farko.
Gwamnan wanda ya ce jawabinsa ne na farko a bainar jama’a tun bayan kammala zaɓen fidda-gwani, ya ce daga yanzu babu wanda ya isa ya yi korafin mayar da ‘yan kabilar Igbo saniyar ware saboda halin da dalaget ɗin suka aikata.
“Na yi tarurruka da dama da shugabannin jam’iyyar na jihohi biyar na shiyyar tare da mataimakin shugabanta na kasa.
“Na roki wakilan da cewa maganar ba ta kaina ba ce, halin da ‘yan kabilar Igbo ke ciki a kasar nan.
“Na roke su da su zaɓi duk wani ɗan takara daga Kudu-maso-Gabas domin idan aka zo kirga kuri’u, kada a bar mu a baya.
"Da mun yi hakan, da mun nuna cewa ƴan kabilar Igbo sun cancanta tare da cancantar shugabancin kasar," in ji shi.
Ya nuna takaici kan yadda ya ce dalaget ɗin yankin sun sayar da ƙuri'un su, inda iya dalaget ɗin Ebonyi ne kawai su ka zaɓe shi da sauran su.
“Za su zo daga baya su riƙa yin kiraye-kirayen hadin kan Igbo da manufofinta amma daga yanzu, ajanda daya tilo da na sani ita ce ajandar Ebonyi," in ji shi.