Sanatan Kano ta tsakiya, Rufai Sani Hanga, ya bayar da umarnin a dawo da motocin da aka raba wa shugabannin Jam’iyyar NNPP a ƙananan hukumomin mazaɓarsa, biyo bayan sauya sheƙarsu zuwa Jam’iyyar APC.
Umarnin na ƙunshe ne cikin wata wasiƙa da Sakataren ofishin Sanatan, Injiniya Ibrahim Nakwalli Kawaji, ya sanya wa hannu. A cewar wasiƙar, an raba motocin ne domin ayyukan jam’iyyar NNPP a matakin ƙananan hukumomi, kuma dole ne a mayar da su ofishin Sanatan da ke kan titin Sokoto Road, a Ƙaramar Nasarawa, tsakanin ranakun 28 zuwa 30 ga Janairu, 2026.
Wasiƙar ta bayyana cewa motocin za su kasance a ofishin Sanatan har sai an warware rikicin cikin gida na jam’iyyar, tare da yin kira ga shugabannin da su ci gaba da nuna biyayya da aminci ga NNPP.
Rahotanni sun nuna cewa umarnin ya shafi dukkan shugabannin NNPP na ƙananan hukumomi da ke Kano ta Tsakiya, ciki har da Dala, Dawakin Kudu, Fagge, Garun Mallam, Gezawa, Gwale, Kano Municipal, Kumbotso, Kura, Madobi, Minjibir, Nasarawa, Tarauni, Ungogo da Warawa.
Wasiƙar ta kuma jaddada cewa dole ne a miƙa motocin kai tsaye ga shugaban ofishin Sanatan, Alhaji Shehu Tijjani Usman Tarauni, inda ta nanata cewa motocin mallakin jam’iyya ne, ba na ɗaiɗaikun mutane ba.
Matakin ya zo ne a daidai lokacin da sauyin sheƙa ya girgiza siyasar Kano, bayan da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya koma APC tare da ’yan majalisar dokokin jiha 22, ’yan majalisar wakilai 8, da kuma dukkan shugabannin ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Sauyin sheƙar ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin ’yan siyasa da magoya bayan jam’iyyun daban-daban. Wani mai amfani da kafafen sada zumunta, Sani Gilashi Haruna, ya soki umarnin Sanatan, yana mai cewa ba shi da misali a tarihin siyasar Kano.
Ya tuna da yadda fitaccen ɗan siyasa, Alhaji Abdussalam Abdulkarim (AA Zaura), ya raba motocin ga shugabannin jam’iyya a dukkan ƙananan hukumomi ba tare da neman a dawo da su ba bayan faduwar zabe.
A nasa martanin, AA Zaura ya ce idan Sanata Hanga ya nace kan karɓar motocin, shi kuma a shirye yake ya samar da sabbin motocin da suka fi inganci domin shugabannin jam’iyyar. Kakakinsa, Malam Dahiru Ahmad Maihuddadu, ya bayyana matakin Sanatan a matsayin abin takaici, yana mai cewa bai dace da tafarkin siyasa mai nagarta ba.





