Jakadan Najeriya da aka nada zuwa kasar Mexico, Reno Omokri, ya gargadi tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, cewa zai iya fuskantar rasa goyon bayan siyasa a jiharsa ta haihuwa ta Adamawa idan ya zabi tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa na 2027.
Omokri ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, yayin da yake mayar da martani ga kalaman, Dele Momodu.
Rahotanni sun nuna cewa Momodu, yayin da yake bayani a shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channels, ya ce hadakar tikitin takara na Atiku da Obi za ta iya kayar da Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, a zaben shugaban kasa mai zuwa.
Sai dai Omokri, duk da cewa ya ce yana girmama Atiku, ya bayyana cewa zabar Obi a matsayin mataimakin takara na iya janyo Atiku ya rasa goyon bayan masu kada kuri’a a Arewacin Najeriya, inda ya ce addini da kuma abubuwan da suka faru a tarihi kan yi tasiri wajen yanke shawarar siyasa.
Ya kuma yi ikirarin cewa har yanzu wasu mazauna Adamawa na ci gaba da nuna bacin rai kan yadda Peter Obi ya mayar da martani game da kisan Ahmed Gulak da aka yi a Owerri a shekarar 2021.
An harbe Gulak, wanda dan asalin Adamawa ne, har lahira ne daga wasu ‘yan bindiga a shekarar 2021.
A cewar Omokri, lamarin ya kara tsananta ne sakamakon yadda Peter Obi ya mayar da martani kan kisan wata mata mai juna biyu, Harira Jubril, da ‘ya’yanta, wanda ya faru a Anambra a watan Mayun shekarar 2022.






