Tsohon Shugaban ƙasa IBB Jan Gwarzo ne------Gwamnan Neja

Tsohon Shugaban ƙasa IBB Jan Gwarzo ne------Gwamnan Neja
Tsohon Shugaban ƙasa IBB Jan Gwarzo ne------Gwamnan Neja
Gwamnan Neja kuma shugaban gwamnonin arewa ta tsakiya ( NCSGF) Abubakar Sani Bello ya bayyana tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida a matsayin kuma jan gwarzo da ke da kyakkyawar alkibla ga kasar nan.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taron lakca na kaddamar da littafi kan rayuwar tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida na cikar sa shekaru tamanin da haihuwa a xakin taron tunawa da Justice Idris Legbo Kutigi da ke Minna.
Gwamna Sani Bello, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Alhaji Ahmed Mohammed Ketso, yace Janar xin uba ne kuma kaka a jihar da kasa baki daya.
Yace Janar Babangida uba ne da ya taka rawar gani wajen haxa kan kasa dan samun zaman lafiya da hadin kan kasa, yace a lokacin mulkinsa ya samu nasarori da dama a kasar nan.
Gwamnan ya taya tsohon shugaban kasar murna, ya kuma yi addu'ar samun lafiya, kwarin guiwar cigaban da zai kawo wa kasar bunkasa da walwala.
Shi ma a na shi jawabin, gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, da ya samu wakiltar mataimakinsa Mista David Onoja, ya bayyana Janar Babangida a matsayin soja kuma dattijo wanda ya cancanci shekarun sa, kasar tana anfana da iliminsa da kwarewarsa.
Yace duk da shekarunsa, da yin ritaya daga aikin soja, kasar na anfana da irin salon da yake takawa wajen gina kasa, anfaninsa zai cigaba da wanzuwa ga kasar nan.
Shugaban taron kuma tsohon shugaban kasa, Janar Abdussalam Abubakar, a sakon taya murnarsa, ya godewa Allah akan wanzuwar IBB, ya bayyana cewar tsohon shugaban kasar a mulkin sojan, daga samartakarsa zuwa yanzu yana da tsarin shugabanci mai inganci, wanda ya nemi matasa da su yi koyi da irin kyawawan halayensa.
Ya yabawa majalisar matasan jihar Neja da suka dauki nauyin shirya taron a madadinsa.
A na shi jawabin, tsohon gwamnan Neja, Dakta Mu'azu Babangida Aliyu ya bayyana cewar Janar IBB ya bada gudunmawa wajen kawo cigaba da bunkasar jihar nan da kasar nan.
Ya bayyana cewar rayuwarsa ta taimaka wajen inganta rayuwar al'umma har ma waxanda ba a haiho ba, yace dole a rika tuna shi da kyakkyawan abubuwan da ya assasa.
Daliban makarantar faramaren IBB da ke minna sun shirya taron addu'o'i na musamman ga tsohon shugaban kasar Janar Ibrahim Badamasi Babangida.