Tsohon ɗan majalisa ya buɗe sabuwar kasuwar manoma, Masallacin Juma’a da gidan mai a mazaɓarsa

Tsohon ɗan majalisa ya buɗe sabuwar kasuwar manoma, Masallacin Juma’a da gidan mai a mazaɓarsa

A jiya Juma'a ne Tsohon Dan Majalisar Wakilai, mai wakiltar mazaɓar Ƙiru da Bebeji, Abdulmumin jibrin Kofa, ya ƙaddamar da kasuwar manoma, cibiyar kasuwanci, masallacin Juma'a da gidan mai a garin na Kofa domin.

Da ya ke jawabi bayan ƙaddamar da sabbin gine-ginen, Kofa ya ce ya samar da cibiyar kasuwancin ne domin bunƙasa harkar noma da kasuwanci, a Karamar Hukumar Bebeji, Jihar Kano.

A cewar Kofa, ɗan takarar Majalisar Wakilai a mazaɓar Kiru da Bebeji jam’iyyar NNPP, samar da katafariyar cibiyar kasuwancin ne domin samar da ayyukan yi ga matasa da kuma ƙarfafa zaman lafiya a yankin.

Ya ƙara da cewa, ktafariyar kasuwar, irinta ta farko a Jihar Kano, wacce a ka kwashe shekaru goma ana aikinta, za ta zamo wata hanya ta bunƙasa harkokin noma da kasuwanci a jihar.

Kasuwar, mai ɗauke da shaguna 200, da masallaci mai daukar masallata 5,000 da gidan mai, da kuma babban filin ajiye motocin tirela- tirela masu daukar kaya da ajiyewa sama da guda 100.

Kofa ya bayyana cewa kasuwar na da irin yanayin da a ke buƙata a kasuwancin zamani, inda ya kara da cewa ta na ɗauke da ɗakin hutawa, wurin karbar magani, sannan kuma sun shirya tsaf wajen bada tsaro mai inganci a kasuwar.

Abdulmumin Jibrin Kofa ya kara da cewar  yanzu haka ma’aikata sama da dari biyar ke aiki tukuru a wannan kasuwar kuma duk da haka ana sa ran za’a kara daukar wasu baya ga waɗanda zasu yi dakon kaya da yaran shago da dai sauransu .