Tsaro: Zamfara za ta zagaye makarantun Sikandare 40 da Katanga

Tsaro: Zamfara za ta zagaye makarantun Sikandare 40 da Katanga
Gwamnatin jihar Zamfara a wani shiri na inganta tsaro da kare kayan gwamnati a makarantun Sikandare na fadin jihar kan wannan ta bayar da kwangilar zagaye makarantu 40 da katangar zamani.
Wannnan yunkurin na samar da abubuwan kawata gari tunani ne da za a rika tabbatarwa a mataki-mataki tare da shigo da wasu ƙarin makarantu nan gaba saboda kula da tsaron su.
Kwamishinan ilmin Kimiya da Fasaha na jiha Malam Wadatau Madawaki ne ya ba da sanarwar a wurin wani taro da wata kungiya a ma'aikatarsa ranar Assabar data gabata, ya kara tabbatar da kudirin gwamnati na inganta fannin ilmi a jiha.
Ya fahimci aikin katangance makarantun abun ne da zai kawo natsuwa a tsakanin dalibai, da zama cikin makaranta, babban kuma an yi maganin matsalar tsaro dake wajen makarantun.
Kwamishina ya bayyana cewa kaso na farko ne za a soma da makarantun 40 an zaɓo su ne a bisa cancanta  a la'akari da yanki da masu tsananin buƙata da tsarin makaranta.
"Za a cigaba da aikin a ko'ina har sai kowace makaranta ta samu kulawar da ta dace da ita, a lokacin wannan gwamnati.
"Muna kira ga masu ruwa da tsaki da jagororin al'umma da masu son cigaban ilmi da su hada kai da gwamnati a tabbatar da daurewar ilmi da wannan aikin da aka ɗauko," a cewar Malam Wadatau.