......kuma daga bisani za ta iya zartas da shi a karatu na biyu.
Hakan ya fito fili ne a ranar Larabar da ta gabata lokacin da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Jibrin Barau, wanda ya jagoranci zaman majalisar ya yi ishara da cewa akwai yiwuwar za a zartar da kudirin a yau (Alhamis).
Bamidele Opeyemi, ya bayyana cewa za a yi muhawara kan kudirin a zauren majalisar ranar Alhamis.
Ya ce, “Za mu saurari kwararrun da za su jagorance mu, domin mu samu damar gabatar da kudirin mu yi muhawara a kansu.
A farkon watan Oktoba ne dai shugaba Bola Tinubu ya mikawa majalisar dokokin kasar wasu kudirori guda hudu na gyaran haraji.
Kafin hakan dai Gwamnoni a Arewacin Nijeriya da sarakuna sun nuna rashin gamsuwarsu da aiwatar da kudirin domin sun zargi kudirin in ya zama doka zai durkusar da yankin Arewa.
Shugaban kasa bai aminta da ra'ayin ba, ya ci gaba da kokarin sai ya tabbatar da kudirin duk da majalisar tattalin arziki ta kasa ta nuna masa rashin amincewarta ga kudirin.
Hakan ya raba kan mutane da dama wasu naganin alfanun tabbatar da kudirin wasu na ganin wani yanki ne zai cutu matukar lamarin ya tabbata.
Daga Abbakar Aleeyu Anache