Tsadar rayuwa:Matasa sun yi zanga-zanga a Sakkwato

Tsadar rayuwa:Matasa sun yi zanga-zanga a Sakkwato



Matasa da yawa sun yi zanga-zangar lumana a birnin Sakkwato ranar Talata data gabata kan matsi da tsadar rayuwa da suke ciki.
Matasa da suka kunshi Maza da mata sun yi  tattaki  har zuwa Gidan gwamnatin jiha suna rike da kwalaye tare da rubutun "yunwa za ta kashe mu" "ya isa hakan" "Muna bukatar abinci".
Safiya Sa'idu tana cikin masu zanga-zangar ta ce ba su fito ne domin cin zarafin kowa ba sai dai suna bukatar a yi Wani abu da sauri don rage matsin da ake fama da shi.
"Kwanon shinkafa ta gida naira 3,800, Garin kwaki 1500 ba zamu lamunce haka ba.
"Mutane suna mutuwa kan yunwa da wuya ka samu gidan da ake girka abinci sau uku a rana.
"Muna son aurar da yaranmu amma komi ya yi tsada a yanzu, yakamata gwamnati ta duba kokenmu ta yi wani abu da sauri," a cewarta.
Muhammad Kamilu ya yi kira da gwamnati ta samar da abinci cikin sauki ga mutane.
"Albashi baya wadatar da mutane a yanzu ga kuma komai ya yi tsada dayawan magidanta ba su iya ciyar da gidansu."
Yusuf Kabiru ya roki gwamnatin tarayya ta mayar da tallafin man fetur shi kadai ne abin da zai samar da sauki ga talaka.