Tsadar rayuwa: Talakawa na shan wahala--Bafarawa

Tsadar rayuwa: Talakawa na shan wahala--Bafarawa

 

Tsohon Gwamnan Sokoto Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya yi kira ga shugabanni a Nijeriya da Sakkwato da su dubi halin da talakawa suke ciki namatsi da wahala, akwai bukatar fito da hanyoyin samun sauki ga mutane.

Attahiru Bafarawa a hirarsa da manema labarai a Saokoto  ya ce lokaci ya yi da yakamata shugabannin su tashi tsaye don magance matsalar da ake ciki mutane suna shan wahala, ana shan wahala, ana shan wahala.
Bafarawa ya roƙi shugabanni su ji tsoron Allah su yi wa talakawa adalci ana fama da ƙarancin abinci da matsalar tsaro, Arewa na ci baya kullum bai dace shugabanni su rungumi hannayensu ba, su tashi tsaye don tsamo mutane daga cikin halin da suke ciki.