Tinubu zai mayar da Gwamna Fubara kan kujera amma da sharadin ba zai nemi tazarce ba - Rahoto 

Tinubu zai mayar da Gwamna Fubara kan kujera amma da sharadin ba zai nemi tazarce ba - Rahoto 

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da mayar da Siminalayi Fubara a matsayin Gwamnan Jihar Rivers — amma da sharadin cewa ba zai sake tsayawa takarar shugabancin jihar a 2027 ba, kamar yadda rahoton TheCable ya bayyana.

An cimma wannan yarjejeniya ne a wani taro da aka gudanar a daren Alhamis a fadar shugaban ƙasa, inda Tinubu ya karɓi bakuncin Nyesom Wike, Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT); Gwamna Fubara; Martin Amaewhule, shugaban majalisar dokokin jihar da aka dakatar; da wasu ‘yan majalisa.

Majiyoyin fadar shugaban ƙasa sun bayyana wa TheCable cewa wannan mataki wani ɓangare ne na ƙoƙarin da ake yi don dawo da tsarin dimokuraɗiyya a Jihar Rivers, kuma yana kunshe da gagarumin yarjejeniya da sauye-sauye.

Bisa bayanan da suka fito daga cikin masu ruwa da tsaki, ɗaya daga cikin muhimman sharuɗɗa shi ne a ba Fubara damar kammala wa’adinsa na shekaru huɗu, amma ya hakura da kowanne yunƙuri na neman wa’adi na biyu a 2027 — wani mataki da zai rage masa ƙarfi a siyasa, amma ya amince da shi.

Wata majiya ta bayyana cewa a cikin yarjejeniyar, Wike zai sami damar zaɓar dukkan shugabannin ƙananan hukumomi guda 23 na jihar.

Majiyar daga fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa hakan zai ba Wike babbar dama a siyasa, musamman wajen riƙe ikon siyasa daga tushe a matsayin Ministan Abuja.

TheCable ta kuma gano cewa Fubara ya amince da biyan dukkan hakkokin da ake bi na ʼyan majalisar jihar guda 27 da suka goyi bayan Wike waɗanda aka dakatar.

A sakamakon haka, ‘yan majalisar ba za su ƙaddamar da yunƙurin tsige Fubara daga mukaminsa ba.