Tinubu zai kammala tantance hidikwatar ƙananan hukumomi 774 na Nijeriya a 2027
Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta sanar da cewa za ta kammala tantance hedkwatar kananan hukumomi 774 a fadin jihohi 36 nan da shekarar 2027.
Ministan sadarwa, kirkire-kirkire, da tattalin arzikin dijital, Dokta Bosun Tijani, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a wani taron masu ruwa da tsaki na komawa kan Project 774 Connectivity a Abuja.
Tijani ya bayyana cewa za a gudanar da aikin ne tare da hadin gwiwar wasu hukumomi da ke karkashin ma’aikatar.
Ya bayyana cewa gwamnati na da burin ganin ta nada dukkan sauran kananan hukumomin kasar nan da shekarar 2027.
Abbakar Aleeyu Anache
managarciya