Tinubu za mu zaɓa a 2027 - Sarkin Daura

Tinubu za mu zaɓa a 2027 - Sarkin Daura

Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Umar, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya kasance zabin da Masarautar Daura ta fi so a zaben shugaban ƙasa na 2027.

Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya tarbi Mai-ɗakin Tinubu, Sanata Oluremi Tinubu, wadda ta jagoranci tawagar matan ƴan majalisu da ministoci don ziyarar ta’aziyya zuwa gidan marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a Daura, Jihar Katsina, a jiya Asabar.

Ta yi wa A'isha Buhari da iyalin marigayin gaisuwa tare da ziyartar kabarin da, inda daga bisani ta wuce gidan Mamman Daura, dan uwa kuma shaƙiƙin Buhari.

A fadar Sarkin Daura, Uwargidan Shugaban Ƙasa ta mika ta’aziyya ga Masarautar bisa rashin ɗaya daga cikin ‘ya’yanta mafi girma da kima.

The Guardian ta rawaito cewa a wani gagarumin nuna goyon baya, Sarkin ya yabawa shugabancin Shugaba Tinubu tare da tabbatarwa Sanata Tinubu da cewa Daura za ta ci gaba da kasancewa cikin sahu na amintattu da masu biyayya ga gwamnatin Shugaban ƙasa, musamman gabanin babban zaɓen 2027.

“Shugaba Tinubu shi ne zabin mu a 2027,” in ji Sarkin. “Muna nan daram a bayansa kuma za mu ci gaba da mara masa baya don ya samu nasara. Tinubu, Tinubu, Tinubu shine zabin mu a 2027," in ji Sarkin.